A Riƙa Sa Masu Cutar Karya Garkuwar Jiki (HIV) Cikin Tsarin Auren Gata Na Gwamnatin Kano -Bashir Isma’ila Kabawa

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An shawarci gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa a shirin da take na sake yin auren gata na mutum 2000, ta yi amfani da iyayen ƙasa, hakimai, dagatai da masu unguwanni a tafi cikin unguwanni da ƙauyuka a duba su wane ne auren ya ƙi yiwuwa saboda rashin kayan ɗaki a zaƙulo su a taimaka musu.

Bashir Isma’ila Kabawa Babban Darakta na Gidauniyar SAVE LIFE SUSTAINABLE AND CONSULING INITIATIVE, wato Gidauniyar Inganta Rayuwa da Ba Da Shawarwari Daga Tushe ne ya ba da wannan shawarar a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya ce auren da aka yi zuwa ake a nemo mutane da a cikinsu wasu ma da dama suna da halin da za su yi a ba su kayan ɗaki da jari da kayan abinci a ce an yi auren, amma ba cewa yake abin da ake ba shi da kyau ba,, shawara ce dai yake ganin wannan hanyar ya kamata a bi ta amfani da iyayen ƙasa a zaluƙo yara marayu da masu iyayen da ba su da hali a bi hanyar da duk ya kamata a bi a yi auren.

Babban Darakta na SLSACI, Bashir Isma’ila Kabawa ya ƙara da yin kira da cewa ko a mutane da suke taimakawa masu larurar cutar nan mai karya garkuwar jiki (HIV), akwai matakin da ya kamata a bi na sirri domin su ma su riƙa amfanar da auren da gwamnatin Kano take, don ba zai yiwu kana da larurar ka zo ka ce kana da ita ba.

Ya ce akwai hanyoyi da ya kamata gwamnati ta bi da za a shigo da waɗannan bayin Allah abu ne da ba za a gaya wa duniya shi ba, amma dai in gwamnatin ta buƙaci hakan akwai hanyoyin da ya kamata su faɗa da za a shigo da masu larurar HIV saboda su ma suna da buƙata sosai da a yanzu ma za su iya kawo mutum 50 a ɓangarensu.

Bashir Isma’ila ya ce sun kafa Gidauniyar ne saboda mutane masu larura mai karya garkuwar jiki don kore musu tsangwama, kuma su ba su taimako da za su iya ba su a kan waɗannan.

Ya ce abin da ya jawo hankalinsu akwai wani da suke tare da shi ɗan unguwar Makafin Dala tsawon shekaru yana gwagwarmaya a cikin waɗannan bayin Allah yau da gobe in za a yi taro yana kiran sa su tafi sai ya kalli irin fama da tsangwama da ƙyama da ake musu a cikin al’umma, don haka ya ga dacewar ya dawo inda yake don samar da wannan ƙungiya domin suna da irin waɗannan mutane a cikin al’umma don a riƙa taimaka musu.

Ya ce shekaru huɗu ke nan da yi wa Gidauniyar rijista sun soma ayyuka ne daga matakin ƙaramar hukumar Dala har ta bunƙasa ta zama ta matakin jihar Kano har ma da wasu jihohi suna aikin tallafa wa bayin Allah suna kuma samun nasarori suna haɗa aurratayya a tsakanin musu larurar.

A baya su suke zuwa da kansu su nemo su, amma an sami cigaba suna zaune wani zai zo tsakanin maza da mata ya ce yana da larurar a nemo masa mai larurar don su yi aure.

Ya yi nuni da cewa, “An sami cigaba sosai saɓanin da, don gudun kar a gane kana da larurar, mutum sai ya ɓoye kansa, kuma ba a damu da gwaji ba. Mace za ta je ta auri wanda yake lafiya, ko shi namiji ya auri mai lafiya a zo a haɗu, maimakon a rage yawan yaɗuwarta, sai ya ƙaru. Yanzu an sami cigaba yadda al’umma ke iya zuwa su ce suna da larurar a haɗa su da mai irin larurar su aura. A haka mun haɗa aure sama da 100.”

Babban Darakta na Gidauniyar SLSACI
ya ce, daga ƙalubale da suke fuskanta shi ne da suna haɗa aure na masu ɗauke da larurar cutar mai karya garkuwar jiki, amma yanzu wani yanayi ya sa kowa da mai larurar da wanda ba shi da ita suna zuwa neman aure, kuma a matsayinsu na masu haɗa aure suna fuskantar ɓacin raini da yi musu wani kallo na rashin daraja, wanda kuma wannan aiki ne da suke saboda Allah da kyakkyawar manufa ga al’umma.

Ya kuma ƙara da cewa, “Har yanzu tsangwamar da ake yi wa masu larurar cuta mai karya garkuwar jiki ba ta ragu ba a cikin al’ummarmu, domin mutanenmu an kasa wayewa a gamsu cewa tunda Allah ya ƙaddara mutum ya sami larurarar a kula da shi da kyautatawa su yi masa fatan samun waraka.”

Bashir Isma’il Kabawa ya ce a ayyukan da suke ba su taɓa samun wata kulawa daga ɓangaren gwamnatin jihar Kano ba, balle shugabannin ƙananan hukumomi duk da sun rubuta takardu da dama zuwa kusan dukkan ƙananan hukumomi na ƙwaryar Birnin Kano guda bakwai, amma ba wani da ya ba su kulawa da za a haɗa kai don tallafawa ƙoƙarin da suke kan masu larurar.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength