Daga Ibrahim Muhammad Kano
Shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Dawakin Kudu (KASSOSA), aji na 1984, Alhaji Garba Ibrahim El-Sulaiman, ya yaba da jajircewar gwamnatin jihar Kano wajen ɗaukar ilimi a matsayin ginshiƙin cigaba, musamman yadda ta ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar ga ɓangaren ilimi.
Alhaji El-Sulaiman ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ’yan jarida, inda ya ce wannan mataki na nuna irin damuwar da gwamnatin Kano ke da ita wajen farfaɗo da ilimi da kuma gina ingantaccen makoma ga matasa.
Ya ce ya zama wajibi a gode wa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da ’yan majalisar dokoki, bisa haɗin kai da suka nuna wajen tabbatar da kasafin da ya bai wa ilimi fifiko na musamman.
Shugaban KASSOSA ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta ƙara haɗa hannu da ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, yana mai nuni da cewa a halin yanzu yawancin farfesoshi da manyan malamai a jami’o’i, har da waɗanda ke koyarwa a ƙasashen waje, tsofaffin ɗaliban makarantun Kimiyya ne.
A cewarsa, yana da matuƙar muhimmanci a riƙa jawo hankalin irin waɗannan ƙwararru idan ana tsara manufofi ko shirye-shirye na bunƙasa ilimi, domin su bayar da shawarwari da gudunmawa ta ilimi da gogewarsu, wanda hakan zai haifar da gagarumin ci gaba.
Alhaji Garba El-Sulaiman ya ƙara da cewa jihohin Kano da Jigawa ya kamata su zama fitila ga Arewa, domin sune za su iya jagorantar yankin wajen fita daga matsalar ƙarancin ilimi, ta hanyar ingantattun manufofi da haɗin gwiwa.
Ya yaba da gudunmawar da ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai ke bayarwa a matakai daban-daban, tun daga tallafin kayan koyo na zamani kamar na’urorin kwamfuta, zuwa sauran abubuwan da ke taimakawa rayuwar ɗalibai a makarantun kimiyya.
El-Sulaiman ya jaddada cewa haɗin kai da gwamnati yana da muhimmanci, kasancewar ita ce ke da ikon tsara doka da manufofi.
A cewarsa, doka ce ta haifar da kafuwar makarantun Kimiyya a baya, kuma doka ce ta ba su damar fitar da ɗaliban da duniya ke alfahari da su a yau.
Ya bayyana fatan a ci gaba da jin ɗaliban jihohin Kano da Jigawa suna haskakawa a fagen ilimi a faɗin duniya.
A ƙarshe, ya ce gwamnatocin jihohin Kano da Jigawa sun nuna ƙwarin gwiwa wajen tallafa wa ilimi, abin da ya rage shi ne a ƙara ƙarfafa musu guiwa.
Ya bayar da shawarar a haɗa uwar ƙungiyar makarantun Kimiyya ta ƙasa da kuma tsofaffin ɗaliban ajujuwa daban-daban, musamman waɗanda suka zama manyan shugabanni da masana a jami’o’i, domin a samar da ingantacciyar mafita ga ƙalubalen ilimi a jihohin Kano da Jigawa.








