Bunƙasa Ilimin Fasaha Zai Taimaka Wajen Samar da Ayyukan Dogaro da Kai In Ji Injiniya Umar Faruk

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Injiniya Umar Faruk, ɗan aji na shekarar 1992 a Kwalejin Fasaha ta Ungogo, kuma jigo a ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda ya ga ci gaba mai kyau a taron ƙungiyar na ƙarshen wannan shekara, idan aka kwatanta da na bara.

Ya ce taron na wannan shekara ya zo da sauye-sauye masu yawa, inda aka samu gyare-gyare a sassa daban-daban na makarantar, sakamakon shigowar gwamnati da kuma fara aiwatar da ayyukan ci gaba a fannin fasaha da koyarwa.

Injiniya Umar Faruk ya yaba da jajircewar tsofaffin ɗalibai daga ajujuwa daban-daban, inda ya ce sun dage wajen bayar da gudunmawa ta hanyoyi iri-iri, lamarin da ke ƙara haɓaka cigaban makarantar da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin ‘yan ƙungiyar.

Ya yi tsokaci da cewa, duk da ƙoƙarin da ake yi wajen bunƙasa harkar ilimin fasaha a wannan lokaci, yankin Arewa ya ɗan fuskanci koma baya a baya.

Sai dai ya nuna ƙwarin gwiwa cewa nan gaba, sannu a hankali, za a riƙa samun ci gaba mai dorewa a fannin fasaha, musamman ta hanyar samar da sana’o’in dogaro da kai.

A cewarsa, gwamnati ta fahimci cewa babu wani fanni da ya fi dacewa a ba da goyon baya kamar na fasaha da ƙere-ƙere, domin shi ne ginshiƙin samar da ayyukan yi.
Wannan, in ji shi, zai taimaka wa gwamnati wajen rage nauyin rashin aikin yi da kuma matsalolin tsaro da hakan ke haifarwa.

Injiniya Umar Faruk ya kuma yaba da ƙoƙarin da ake yi na haɗa dukkan rassan ƙungiyoyin tsofaffin ɗaliban makarantun fasaha na jihar Kano ƙarƙashin inuwa guda, domin samar da sauƙin aiki tare, tallafawa juna, da kuma bunƙasa cigaban makarantun fasaha a jihar baki ɗaya.

  • Related Posts

    Mataimakin Gwamnan Kano Ya Halarci Taron Maulidin Manzo (S) da Hon. Muktar Ishaq Ya Saba Shiryawa A Yakasai

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Murtala Sule Garo, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa, da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad…

    Iyayen Yara Sun Yaba Wa Makarantar Al-Burhan International College Bisa Yaye Mahaddata Al-Qur’ani Karo Na Huɗu

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Al-Burhan International College da ke Bayan Wailaki a Jihar Kano, ta gudanar da bikin yaye mahaddata Al-Qur’ani karo na hudu. Da yake bayani kan kafuwar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength