Daga Ibrahim Muhammad
Mambobin jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kano, sun bayyana ranar da ‘yan takarar majalisar wakilai ta tarayya da na jiha a zaɓen shekarar 2023 ƙarƙashin tutar jam’iyyar za su gudanar da taron masu ruwa da tsaki.
Taron da aka shirya gudanarwa a Lahadi, 12 ga watan Yuli, ya zama wani muhimmin mataki ne domin magance rikice-rikicen da sanin makomar jam’iyyar reshen Kano.
Taron na masu ruwa tsakin da zai gudana ƙarƙashin jagorancin Ambasada Abdul Rahman M. Salga Mainasara, shugaban zauren ‘yan takarar, kuma tsohon ɗan takarar majalisar wakilai ta tarayya na ƙaramar hukumar Dala a zaɓen 2023, na da nufin tattauna alƙiblarsu da ƙawancen da za su yi a gaba.
Muhimmin tsare-tsaren taron dai shi ne yanke shawara kan sakamakon bincike dangane da yadda ake ƙara samun rashin haɗin kai da kuma nuna damuwa kan ayyukan da ake zargin jam’iyyar da yi na ruguza tsarin PDP na jihar Kano tun bayan zaɓen 2023.
A wata tattaunawa ta musamman, Ambasada Mainasara ya bayyana cewa, “Bayan binciken ƙwaƙwaf, mun gano cewa shugabannin jam’iyyar PDP na jihar Kano suna aiki da ministan babban birnin tarayya na yanzu, Nyesom Wike, kuma ana zargin Wike yana yi wa jam’iyyar APC mai mulki aiki”.
Wannan tonon silili dai ya tayar da hankula a tsakanin masu goyon bayan jam’iyyar da kuma ‘yan takarar 2023. Da dama daga cikinsu sun bayyana rashin jin daɗinsu kan abin da suke ganin cin amana ne da zagon ƙasa daga cikin gida.
Hon.Ambasada Abdurrahman Mainasara ya yi gargaɗin cewa dole ne jam’iyyar ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki domin kare martabarta da kimarta a jihar Kano. “Ba za mu iya barin wasu marasa kishi su mallaki ƙasarmu ba. Don haka ya kamata mu fito mu yi yaƙi domin kare rayuwarmu.”
Ya ƙara da cewa wannan mataki ne da zauren ‘yan takarar ke da shi na kishi kan makomar PDP a jihar Kano.
Taron na masu ruwa da tsakin zauren ‘yan takarar ‘yan takarar mai zuwa zai zama wani dandali na tsara hanyoyin da za a bi.
Shawarwarin da aka cimma a ranar taron za su zama ginshiƙin haɗin kai da kuma makomar ‘ya’yan PDP a Kano.
Masu lura da al’amuran siyasa na zura ido a kan waɗannan abubuwan da ke faruwa, inda suke kallon matakin na zauren ‘yan takarar na jam’iyyar PDP na iya sake fasalin jam’iyyar a cikin siyasar Nijeriya.
Yayin da jam’iyyar PDP ke cigaba da kokawa kan rigingimun cikin gida a faɗin ƙasar nan, za a sa ido a kan jihar Kano a ƙarshen makon nan.
Abin jira a gani shi ne yadda zauren ‘yan takarar majalisar tarayya da na jiha a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 zai tafiyar da ‘ya’yan jam’iyyar zuwa ga haɗin kai da sabunta manufa, amma abu ɗaya a bayyane yake: “Ginshiƙin jam’iyyar PDP a Kano ba shi da tushe.”






