Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Mutum 1,360 daga jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Kumbotso da ke jihar Kano ne suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NDC mai tafiyar Kwankwasiyya a makon da ya gabata.
Madugun tafiyar Kwankwasiyya, kuma mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ne ya tarbe su a gidansa da ke kan titin Miller Road a Kano.
Da yake ƙarin haske kan sauya sheƙar, shugaban Caucus na NDC Kwankwasiyya a ƙaramar hukumar Kumbotso, Ambasada Hon. Isyaku Yahaya Talba, ya bayyana cewa waɗanda suka koma jam’iyyar sun yi hakan ne bisa gamsuwarsu da amana, kyakkyawan tsari, ɗabi’a da aƙidar ci gaban al’umma da tafiyar Kwankwasiyya ta ƙunsa.
Ya ƙara da cewa al’ummar Kumbotso sun aminta da jagorancin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a cewarsa, babban burinsa shi ne ganin al’umma sun samu ci gaba da kuma sauƙin rayuwa.
Ambasada Talba ya bayyana cewa amana da nagartaccen jagorancin da suke nunawa a tafiyar Kwankwasiyya a Kumbotso ne suka sa, a cewarsa, al’umma suke mara musu baya.
Ya kuma yi albishir da cewa nan ba da daɗewa ba, za a samu ƙarin mutane da yawa da za su sauya sheka zuwa tafiyar Kwankwasiyya, yana mai cewa ana sa ran adadin zai ninka wanda aka samu a wannan karon.






