Dag Ibrahim Muhammad Kano
Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa masa lamba ya yi takara, har ma suka sayo masa fom din takara saboda sun ga cancantarsa.
Dakta Bashir ya ce, idan aka duba irin siyasar Jihar Kano ta tsarin ubangida, ko da mutum yana da gogewa, cancanta da iya aiki, ba zai iya samun takara a manyan jam’iyyu ba matukar ba shi da ubangida ko kuma ba shi da kuɗi.
Ya ce wannan ne ya sa al’ummar Gwale ke neman sauyi, inda suka ga ya dace su shiga jam’iyyar ADP mai dauke da akidar ci gaba, domin talaka ya mike kafa, ya samu ‘yanci da kuma samun wakilci na gari.
A cewarsa, jam’iyyar ADP mai alamar Littafi, za ta ba ilimi kulawa ta musamman, sannan tana da tsare-tsare na inganta harkar lafiya, gina al’umma da kuma sauraron bukatun jama’a.
Ya koka kan yadda al’ummar Gwale ke da matsala da ‘yan majalisar da suke zaɓa. Ya ce, da zarar sun ci zaɓe ba sa sake dawowa sai idan wani zaɓen ya matso. A baya, ko a waya ko a fili, talakawa ba sa samun damar ganinsu.
Don haka, ya ce a tsarinsu da manufarsu, za su kasance tare da jama’a kullum. Za su bude ofishin dan majalisa na musamman domin karbar korafe-korafen al’ummar Gwale daga ranar Litinin zuwa Juma’a, wanda zai rika sadar da shi da jama’a a koda yaushe. Duk matsalar da za a iya warwarewa a take na ‘yan Gwale, za a warware ta a take.
Ya kara da cewa, abin da ba za a iya yi a lokacin ba, za a yi masa tanadi har sai an samu dama a aiwatar da shi. Sannan za su samar da dandalin tattaunawa (forum) na jama’ar Gwale wanda zai hada ‘yan boko, malaman addini, masu sarautun gargajiya, kungiyoyin neman ci gaban al’umma, da kuma matasa maza da mata, domin tattauna matsalolin al’umma da kawo su majalisa domin magance su da kyautata rayuwar al’umma.
Dakta Bashir Aliyu Galadanci ya yi kira ga al’ummar Gwale da su farka daga barcin da suke ciki, su daina zabar jam’iyyar ubangida. Ya ce duk wadanda ake zaba a yanzu, wasu ne suka kawo su, ko dai ‘yayan wane ne ko dan gidan wane ne. Wannan ne dalilin da ya janyo halin da ake ciki na rashin samun kyakkyawar wakilci.
Don haka, ya bukaci jama’a da su farka, su ajiye maganar jam’iyya su zabi cancanta, su zabi dan takarar da yake tsaye da kafarsa, ba dan gidan kowa ba, su zabi wanda ya damu da damuwarsu kuma zai ba su wakilci na kwarai.






