Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Barrister MB Shehu, ya ce ba za su lamunci duk wani yunƙurin lalata fastoci da allunan tallan jam’iyyar APC a faɗin ƙaramar hukumar ba.
Hon. MB Shehu ya bayyana hakan ne yayin rabon tallafi ga magoya bayan jam’iyyar APC a Fagge, inda ya ce sun amince da ƙalubalen duk wanda yake ganin zai iya tunkarar su a fagen siyasar ƙaramar hukumar.
Ya ce, “Duk wanda ya lalata mana fasto guda ɗaya, za mu mayar da martani ta hanyar lalata guda dubu. Za mu kare martabar jam’iyyar APC da shugabanninta.”
Ɗan Majalisar ya kuma yi kira ga magoya bayan APC da su kasance masu tsayin daka wajen kare mutunci da martabar jam’iyyar, yana mai zargin wasu ’yan adawa da ƙoƙarin lalata hotuna da allunan tallan APC a sassa daban-daban na Fagge.
Hon. MB Shehu ya jaddada cewa APC ta samu gindin zama mai ƙarfi a Fagge, yana mai cewa ba za su bari a rusa abin da suka gina ba.







