Daga Ibrahim Muhammad
An ƙaddamar da littafin Dala’ilul Khairatti na Shehu Jazuli, wanda Nura mai Dala’ilu na Malam Abdul -Yassar ya tarjama daga Larabci zuwa rubutun Hausa.
Taron ƙaddamar da littafin an gudanar da shi ne a ɗakin taro na Kwalejin Nazarin Harkokin Shari’ar Muslunci na Aminu Kano a ranar Asabar.
Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ƙaddamar da littafin na tarjaman Dala’ilun marubucin littafin, Malam Muhammad Nuruddeen Aminu AbdulRahman da aka fi sani da mura mai Dala’ilu, wanda ɗan asalin unguwar Kwalwa ne gidan makaranta a birnin Kano ya ce karatun Dala’ilul Khairatti suna yin sa ne tun daga goyo zuwa mutuwa, domin sun taso ne sun sami da’irorin a kewaye da su na karatun Dala’ilu.
Ya ba da misali da cewa a lokacin da suke kananan yara ma in sun yin sa da ba a san inda suka tafi ba sun yi laifi za a yi musu wani abu, idan suka ce daga makarantar Dala’ilu suke sai a ƙyale su. “Tun daga yarinta muka gano idan muka fake da Dala’ilul Khairati akwai ceto a ciki,” in ji shi.
Malam Nura Mai Dala’lu ya ce, wasu daga abokansu ma sun haddace Dala’ilu, su kuma da ba su sami baiwar haddar ba, amma baya alfahari, idan mutum yana karatun Dala’ilu duk da ba shi da haddar, amma idan ya yi tuntuɓen wasali zai gyara masa ya ce ba haka wajen nan yake ba. Don haka suna gode wa Allah da wannan baiwa da ya yi musu.
Ya ce yana da kyakkyawan zato tarjaman Dala’ilun na Larabci da Hausa da ya yi zai taimaka wa mutane, musamman shi da yake a cikin gari, kuma makarantu suke kewaye da su, a gidansa ma akwai makarantar Dala’ilu suna so yara tunda Allah ya sa yanzu akwai ilimin boko a ko’ina yara ma za su iya karantawa da kansu.
Ya yi nuni da cewa yanzu sanin ilimin Arabiyya ya zama sai ɗan gata don wanda za a tsayawa ya yi karatun Allo ya fahimci addini sai ɗan gata saboda haka ya yi kira ga iyaye su yi tsayin daka wajen su ga ‘ya’yansu suna karanta Dala’ilu don kwai tsira sosai a cikin sha’anin salatin Annabi (SAW), shi jiyau ne, kuma ganau ne, tunda ya soma, kusan shekaru biyar bai taɓa girgiza ba, yana godiya ga Allah.
Malam Nura Mai Dala’lu ya ce ranar da tafi yi masa farin ciki a rayuwarsa ita ce ranar da ya ziyarci Annabi Muhammad (SAW), sai kuma wannan rana da yake farin ciki da ita ta ƙaddamar da wannan tarjama na Dala’ilul Khairati da ya yi al’umma suka taru a kan wannan aiki da Allah ya ƙaddara zai zama ta ƙarƙashinsa yana mutuƙar godiya ga Allah kan wannan.
Da yake zantawa da ‘yan jarida Malam Abdulƙadir Shehu Mai Anwaru da ya wakilci Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai Khadimul Nabiyyi a taron ya gabatar da sayen littafin a kan ₦500,000 ya ce ya cika da farin ciki kamar yadda shi ma wanda ya wakilta yake farin cikin an gayyace shi hidimar salati ga Annabi, amma saboda wani uzuri na ɗaurin aure bai samu zuwa ba ya turo shi.
Ya yi nuni da cewa mutane sun san littafin Dala’ilul Khairati shi ne mafi shahara a duniya da ya ƙunshi nau’oi iri-iri na salatin Annabi. “Tasirin mayar da shi da Hausa zai sa yara su fahimce shi cikin sauƙi domin tun suna yara ake kai su boko sun iya karatu,” in ji shi.
Mai Anwaru ya ce a da sai ka iya Larabci za ka iya karantawa, amma yanzu ko ba ka iya Larabci ba in dai ka yi boko za ka ɗau Dala’ilu da wannan tarjama da aka yi masa da mayar da rubutunsa da Arabia zuwa Hausar boko ka iya karantawa.







