Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana haƙƙin iyaye da za su bai wa ‘ya’yansu shi ne na farko ka ba shi tarbiyya. Na biyu kuma ka ba shi ilimi mai albarka da al’umma za su amfane shi da yin alfahari da shi.
Ɗaya daga cikin iyayen yara a yayin taron saukar karatu da raba kyautuka na makarantar Al-Azhar da ke Kano, Alhaji Adamu Ibrahim ɗan kasuwa a Kano a kasuwar titin Beirut ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida ya ce a matsayinsu na iyaye, ya gamsu da tarbiyyar makarantar shi ya sa ma ‘ya’yansa guda bakwai ne suke karatu a ciki idan da a ce babu tarbiyya babu yadda za a yi ya sa su.
Ya bayyana cewa makarantu irin waɗannan masu zaman kansu na iya ƙoƙarin su wajen tallafa wa cigaban ilimi domin abin ya yi ya wa gwamnati ita kaɗai ba za ta iya gamsar da al’umma gaba ɗaya da ilimi ba. Duk da ba kowa ne zai kawo ɗansa makarantar me zaman kanta ba, amma yana da kyau a riƙa dubawa ana taimaka wa waɗanda ba za su iya kawo ‘ya’yansu ba.
Alhaji Adamu Ibrahim ya yi kira makarantu masu zaman kansu su ƙara zage damtse su faɗaɗa ƙoƙarinsu, musamman wannan makarantar ta Al-Azhar, kuma suna mutuƙar jin daɗin yadda masu makarantar ke karɓar shawarwarin iyaye idan suka hango wani gyara da suka ga ya kamata a yi.







