An Nemi ‘Yan Jarida Su Tsaya Kan Ƙa’idojin Aiki

Daga Ibrahim Muhammad

Yunƙurin razana ɗan jarida da Kwamishina Yaɗa Labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya ya yi a sakamakon gudanar da aikinsa bisa tanadi na dokar aikin jarida ta sa mutane na yi masa kallo alamun gazawa wajen sanin nauyin da ya rataya a kan ɗan jarida.

Cikin irin waɗannan mutane akwai wani tsohon fitaccen ɗan jarida a Kano da ya yi aiki a jaridu daban-daban a faɗin kasar nan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, daga furucin da Kwamishinan Yaɗa Labaran ya yi wa ɗan jaridar na cewa, “Wane irin aikin jarida kuke yi? Me ya sa kuka kasa barin wannan batu ya mutu.” Ya nuna mutuƙar rauninsa na sanin aikin jarida.

Ya yi nuni da cewa shi ɗan jarida yana aiki ne ba don ra’ayin wani mai mulki ba. Yana wakiltar al’umma ne, ya kare gaskiya ya wayar da kai, kuma ya fallasa abin da ka iya cutar da mutane. Muddin yana yin aiki ne a kan doron ƙa’ida ta aikin da gaskiya da amana.

Ya ƙara da cewa ya cika da mutuƙar mamaki a kan kalaman Kwamishinan da ya kamata a ce ya bambanta da tsarin ƙungiyoyi da ya fi sani da kuma aikin jarida, don haka ya shawarce shi da ya yi taka-tsantsan da yin irin wannan kalamai da za su sa a ga wallensa don kawai ya kare wani nasa.

Ya ƙara da bayyana cewa shi aikin jarida ba Kwamishina ne ko wani mai mulki ne zai ba shi damar abin da zai faɗa ba muddin yana yin aikinsa ne bisa ƙa’ida da tsare dokokin aikin.

Dan haka ma ya ja hankalin ‘yan jarida a kan kada su kuskura su riƙa ƙin faɗar gaskiya a kan duk wani abu da ya taso kada su karkata su biyewa son rai, yin hakan kaucewa ƙa’ida ne da cin amana na aikinsu. “Kar ku bari wani jami’in gwamnati, ko wani mai riƙe da muƙami ya sa ku bar dokoki da ƙa’idojin aikinku. A maimakon haka ku tsaya a kan gaskiya ita ce kima da mutuncinku,” in ji shi.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo