Daga Ibrahim Muhammad
An yi kira ga matasa a kan su farka su san inda suka sa gaba da sanin inda yake musu ciwo domin yin abin da yakamata don kawo gyara a tafiyar harkokin siyasar ƙasar nan.
Ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Anti Coalition Movement of Nigeria da ke ƙoƙarin nusar da matasa irin rawar da yakamata su taka don tabbatar da siyasa ta cancanta da adalci a tsakanin matasa a ƙasar nan, Kwamared Haruna Wakili ne ya yi kiran.
Ya ƙara da cewa yakamata matasa su gane cewa kamar yadda suka ɗauki tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammad Buhari suka kawo shi da kyakkyawan tunanin cewa zai fitar da kitsen daga wuta da tunanin shi kaɗai ne zai iya kawar da matsaloli ashe cikin rashin sani ba haka bane, domin bai san ma matsalolinsu ba.
Kwamared Haruna Kabiru Wakili, wanda ya yi takarar neman Majalisar Tarayyar na ƙaramar hukumar Fagge a zaɓen 2023 ya ce haka a jihar Kano matasa suka ɗauka ita wannan gwamnati ta Kwankwasiyya ita za ta fitar da su daga matsaloli da ake a ciki na rashin aikin yi da matsalolin yawaitar shaye-shaye da ƙwace waya, ashe shi ma ba haka ba ne rashin sani ne.
Don haka a irin wannan hali yakamata matasa su yi karatun ta-natsu su lura dukkannin dattijan da su suka yi mulki shekaran jiya da jiya sune kuma suke yi a yanzu, ba za su bayar da mafita ba a mukin ƙasar nan.
Ya ce, “Mafita ita ce sai matasa sun haƙura da irin siyasar da ake ta “ku ba a kashe ku ba, ku ba a raya ku ba ana ɗauko ₦10,000, ₦5,000, ₦50,000, ₦100,000 wanda ya yi dace shi za a bai wa miliyan ɗaya don kare muradunsu.
Kwamared Haruna Kabiru Wakili ya ce, “Wannan irin siyasa ta son rai da tumasanci sai matasa sun haƙura da ita gaba ɗaya sun zo an yi siyasa ta aƙida ta kishi da adalci da sanin yakamata. Ta sanin kai a zo a haɗu don samar da shugabanni masu adalci, kishi da sanin haƙƙin al’umma a kowane mataki,” in ji shi.







