Daga Ibrahim Muhammad
Gwamnatin jihar Kano ta ƙaryata labarin da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai da ake cewa an karkatar da Naira biliyan 6.5 daga baitulmalin jihar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwa da darakta janar na yaɗa labaran Gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature DawakinTofa, ya fitar a ranar Litinin ga manema labarai.
Sanarwar, ta ce rahoton da jaridar Daily Nigerian ta wallafa a ranar 22 ga Agusta, 2025, kan daraktan tsare-tsaren Gwamnan Kano, Abdullahi Rogo, labari ne ƙanzon kurege da aka ƙirƙira domin ɓata sunan gwamnatin.
Bature Dawakin Tofa ya yi nuni da cewa duk wani kuɗi da ake fitarwa daga baitulmalin jihar ana yi ne bisa tsarin kasafi, “Babu wani ma’aikaci da ke da ikon sarrafa kuɗin jama’a ba tare da izini ba,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta yi ƙarin haske cewa ofishin gwamnatin jihar ne ke da alhakin gudanar da harkokin sufuri, masauki, tarurruka da kuma karɓar manyan baƙi ciki har da jami’an gwamnati daga Abuja da ƙasashen waje da ake yawan buƙatar kuɗaɗe masu yawa.
Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da gudanar da mulki kan doron gaskiya da riƙon amana, tare da bayar da damar bincike ga hukumomin da suka dace idan akwai buƙata.
Gwamnatin ta yi kira ga jama’a da su yi watsi tare da yin hattara da irin waɗannan labaran bogi da abokan hamayya ke yaɗawa a kafofin sadarwa da nufin rikita jama’a.
Sanarwar gwamnatin jihar Kano ta ce tunda al’amarin yana gaban kotu, ba za ta yi ƙarin bayani ba sai dai a jira hukuncin da kotu za ta yanke hukunci.







