Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana cewa a siyasar ƙaramar hukumar Dala da ke jihar Kano, mutum ɗaya tilo da yake taka rawar gani wajen yin tsayin daka da sadaukar da kansa wajen cigaban al’umma, babu wanda ya kai Hon. Ibrahim Namadi Dala.
Wani matashi Mustapha Isah Ɗandinshe ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ƙara da cewa Hon. Namadi jagora ne mai kishin al’umma, wanda kullum yake faɗa da cikawa da ba ya yin alƙawari na je-ka-na-yi-ka, “Ayyukansa a bayyane suke na nuna halayyar dattaku da ɗabi’u da ya cancanci jagoranci a kowane mataki.” In ji shi.
Ya ce a Dala, suna ganin yadda yake tsayawa da jama’a a lokuta daban-daban yana sauraren bukatunsu, yana tallafa musu ba tare da nuna bambancin siyasa ba, kuma cikin girmamawa. “Hakan ya tabbatar mana da cewa shi jagora ne ba kawai domin siyasa ba,” ya jaddada.
Mustapha Isah Ɗandinshe ya yi fata tare da riƙon Allah ya tabbatar musu da buri da suke da shi na ganin Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala ya zama ɗan Majalisar Tarayya na Dala a 2027 domin ya cigaba da haskaka ƙaramar hukumar da yin jagoranci mai ma’ana.






