Sama Da Mutum 400 Sun Amfani Aikin Idanu Da Gidauniyar Shattima Kankare Ta Ɗauki Nauyi

Daga Ibrahim Muhammad

Ɗimbin jama’a ne daga sassan mazaɓun ƙwaryar Fagge suka amfana da aikin duba idanu da ba su magunguna da Hon. Muhammsd Shattima Kankare ya ɗauki nauyi.

Da yake bayani game da aikin idanun, Hon. Hussain Ibrahim Kote Babban mataimaki ga mataimakin shugaban majalisar Dattawa Sanata Barau I Jibrin, wanda kuma shi ne jagoran tafiyar Hon. Muhammad Shattima Kankare na mazaɓun ƙwaryar Fagge guda biyar ya ce, taro ne na aikin ido da ake ƙarƙashin Gidauniyar Marigayi Shattima, wanda Hon. Muhammad Shattima Kankare mai neman takarar Majalisar Tarayya na Fagge a jam’iyyar APC ya ɗauki nauyi.

Ya ƙara da cewa an kawo likitoci ƙwararru su duba idanun mutane da ke da larura wanda za a yi wa aiki a yi musu, waɗanda za a ba su gilashi a ba su, waɗanda kuma magani ne an ba su.

“A aikin da ake gudanarwa wani ya zo idon ya ƙwaƙule ya fita aka ɗauki za a saka masa wani da zai cike gurbin wajen, wasu kuma aiki aka yi na yana,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa mutane 200 aka yi ƙiyasin za a yi wa aikin idanun, amma da aka zo ana aikin kusan mutum 400 ne suka zo, don haka aka ƙaro kayan aiki domin su ma a duba su.

“Aikin kuma shi ne karo na biyu da aka yi. An yi na farko a Arewacin Fagge mazaɓar Rijiyar Lemo da Kwaciri da ‘Yan Mota Gabas. A can an duba ɗaruruwan mutane a wuni ɗaya tun 7 na safe har zuwa 6 na yamma.

Hon. Hussaini Ibrahim Kote ya ce abin da ya jawo hankalin Hon. Muhammad Shattima Kankare yin irin waɗannan ayyuka da dama na alkhairi a ɓangarori daban-daban shi ne ya gada ne a wajen mahaifinsa, wanda a rayuwarsa mutum ne mai taimakawa al’umma. Don haka shi ma yake don haka tun ma ba shi da wata sha’awa ta neman wata kujera ta siyasa da mutane suka nemi ya yi yake irin waɗannan ayyuka na tallafawa masu ƙaramin ƙarfi da mabuƙata.

Ya ce daga irin tallafi da yake bayarwa akwai na ilimi duk wata sabga da ta shafi ilimi in aka kai gabansa zai taimaka wajen biyawa ɗalibai yin rijista a manyan jami’o’i da manyan makarantu yana taimakawa mata da marayu.

A kwanakin baya ma ya sayawa wasu amare da ba su da hali katifu, wanda shi aka wakilta ya ba su.

Ya ce ba a yin mako guda Hon. Muhammad Shattima Kankare bai ɓatar da kuɗi sama da N400,000 ba ta hannunsa a cikin ƙaramar hukumar Fagge, wanda za a tallafawa mutane mai N50,000,30,20.

“Wannan duk aiki ne da mai neman tsayawa takarar majalisar tarayya na Fagge a APC yake,” in shi.

Hon. Hussaini Ibrahim ya yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Fagge su bai wa Hon. Muhammad Shattima Kankare goyon baya har burinsa ya cika ya zama ɗan takarar Majalisar Tarayyar na Fagge a ƙarƙashin jam’iyyar APC, kuma ya yi nasarar zama ɗan Majalisar Tarayyar da zai mayar da ƙaramar hukumar abar kwatance tsakanin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano wajen cigaba.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum