Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙara kuɗin da ake yi biya don yin fasfo ɗin ƙasa da ƙasa zuwa ₦200k. Ƙarin zai fara aiki ne daga ranar Litinin 1 ga Satumba, 2025.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na Ma’aikatan Shige ta Fice ta Nijeriya, ACI Akinlabi ya sanyawa hannu a ranar Alhamis, ta ce sabbin kuɗaɗen za su shafi aikace-aikacen da ake yi a Nijeriya ne kawai.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Bita da aka yi wanda kawai ya shafi kuɗaɗen neman Fasfo ne kawai da ake yi a Nijeriya, a yanzu ya sanya sabon matakin biyan kuɗi na shafuka 32 tare da tsawon shekaru 5 a kan N100,000 da shafi 64 tare da tsawon shekaru 10 akan N200,000,” in ji sanarwar.
Sabonzu tsarin biyan kuɗi na shafuka 32 da zai yi aiki na tsawon shekaru 5 a kan N100,000 da shafi 64 tare da tsawon shekaru 10 a kan N200,000, ”in ji sanarwar.
Sai dai sanarwar ta fayyace cewa har yanzu ba a canza kuɗaɗen da ake biya na ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ba da suke biyan Dala 150 kan Fasfo mai shafuka 32 da Fasfo na shekara 5 da kuma Dala 230 na Fasfo mai shafuka 64 da shekaru 10.
Hukumar ta ce an yi gyaran ne da nufin kiyaye inganci Fasfo ɗin Nijeriya, tare da tabbatar da isa ga ‘yan ƙasar yadda ya kamata.
Wannan sabon tsarin na zuwa ne shekara guda bayan da Gwamnatin Tarayya ta amince da gyara tun farko a watan Agusta 2024, wanda ya fara aiki daga Satumba 1, 2024.
A lokacin, an ƙara kuɗin littafin Fasfo mai shafuka 32, mai shekaru 5 daga N35,000 zuwa N50,000, yayin da Fasfo mai shafi 64, mai shekaru 10 ya tashi daga N70,000 zuwa N100,000.
Daga nan ne hukumar shige da fice ta bayyana cewa ƙarin ya zama dole don ɗorewar ingancin Fasfo ɗin Nijeriya da kuma inganta harkokin zirga-zirga.







