Allah ya yi wa tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda Solomon Arase rasuwa.
Tsohon shugaban ‘yan sandan ya rasu ne a ranar Lahadi, 31 ga watan Agusta, 2025, a asibitin Cedarcrest da ke Abuja.
Arase ya taɓa zama Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya na 18, kuma ya yi ritaya a shekarar 2016.
Kafin ya zama IGP, ya shugabanci hukumar leƙen asiri da bincike na manyan laifuka, babban sashin leƙen asiri na rundunar ‘yan sanda.
An haifi Arase a ranar 21 ga watan Yuni, 1956, a ƙaramar hukumar Owan ta Yamma a jihar Edo, Arase ya karanci kimiyyar siyasa a Jami’ar Ahmadu Bello, inda ya kammala a shekarar 1980, sannan ya shiga aikin ‘yan sandan Nijeriya a ranar 1 ga Disamba, 1981.
Daga nan ya samu digirin-digirgir a fannin shari’a a Jami’ar Benin da kuma digiri na biyu a Jami’ar Legas.
A lokacin aikinsa, ya riƙe muƙamai da dama da suka haɗa da Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom da mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da harkokin leƙen asiri.
Ya kuma yi aiki a Namibiya a matsayin wani ɓangare na aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma ya kasance memba a Kwalejin Tsaro ta Nijeriya.
Arase ya yi ritaya daga aikin ‘yan sanda ne a ranar 21 ga watan Yuni, 2016, bayan ya kai shekarun ritayar dole.
Marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar ‘yan sanda a watan Janairun 2023.
Shugaba Bola Tinubu ne ya tsige shi daga muƙaminsa a watan Yunin 2024.








