Al’ummar Kano Ku Fito Ku Yi Rijistar Zaɓe Don Kare ‘Yancinku -Jagoran ADC Iyali Ɗaya

Daga Ibrahim Muhammad

Jigo a siyasar ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano, Jagoran Ƙungiyar ADC Iyali Ɗaya, Ambasada AbduRahman Mansur Mainasara Salga ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da Arewa baki daya a kan su fito domin yin rijistar katin zaɓe da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) take yi a halin yanzu.

Ya bayyana cewa a matsayin karamar hukumarsu ta Dala da suke da yawan al’umma, kuma cibiyar siyasa a faɗin ƙasar nan yana da mutuƙar muhimmanci ga duk wanda ya kai munzalin shekarun yin katin zaben da waɗanda nasu ya salwanta su daure su tabbatar sun je an yi musu, domin a wannan tsari na demakraɗiyya da muke a ciki katin zaɓen ne zai zama muhimmin makami da za a yi amfani da shi wajen kaɗa ƙuri’a don kwatar ‘yancinsu.

Jakadan Zaman Lafiya Hon. AbdurRahman Mansur Mai Nasara, wanda ya yi takarar nema ɗan Majalisar Tarayyar a ƙaramar hukumar Dala a zaɓen 2023, ya yi nuni da cewa halin da aka jefa ƙasar nan a ciki na rashin walwala da tsananin ƙuncin rayuwa da barazanar tsaro, al’umma za su iya ƙwatar kansu ne kawai ta amfani da ‘yancinsu na katin zaɓe su jefa ƙuri’a domin kawar da zalunci.

Ya ƙara da cewa a yanzu halinda ake a ciki a jihar Kano da Arewa da ƙasa baki ɗaya ya zama wajibi al’umma su fito duk wanda ya isa mallakar katin zaɓe, musamman matasa maza da mata da iyaye su yi tanadi domin zaɓe mai zuwa da shi za su yi amfani domin samawa kansu alƙiblar shugabanci da zai bunƙasa cigaban rayuwarsu.

Ya ce yanzu daga soma gudanar baikin yin rijistar zaɓen da INEC ta soma bayanai daga wasu jihohin kudancin ƙasar nan da ba su da mutane da yawa mutane na ta tururuwar zuwa yin rijistar sun sami adadin mutane da yawa ninkin ba ninki, amma a jihar Kano da sauran jihohi na Arewa ba sa zuwa yin rijistar da hakan ba ƙaramin haɗari ba ne ga jihar Kano da Arewa.

Hon. AbdulRahman Mainasara Salga ya shawarci al’ummar ƙasar nan a kan su bai wa jam’iyyarsu ta ADC haɗin kai da goyon baya don ganin ta sami nasara a shekara a 2027 don kawo gyara da fitar da al’umma daga matsaloli da ake fama da su a ƙasar nan.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum