Kanawa Ku Fito Ku Karɓi Rijistar Zaɓe Don Fatattakar Gwamnatin Zalunci -Ibrahim Al-amin Little

Daga Ibrahim Muhammad

Fitaccen ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa a jihar Kano, Alhaji Ibrahim Al-amin Little, ya yi kira ga al’ummar jihar a kan su fito domin yankar katin rijistar zaɓe da Hukumar Zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta soma bayarwa.

Ya ce rijistar zaɓen ita ce makami da ‘yancin al’umma wajen fatattakar gwamnatin jam’iyyar APC da ta kawo yunwa, talauci da fatara da rashin tsaro da hanyoyi da ababe more rayuwa.

Alhaji Ibrahim Al-amin Little ya bayyana al’ummar jihar Kano matsayin alƙiblar siyasar ƙasar nan, waɗanda da ƙuri’unsu kaɗai za a iya canza siyasar Nijeriya a samar da shugabanni nagari.

Dan haka ya ce ga jam’iyyar ADC ta fito da ƙarfin ikon Allah domin samar da shugabanci nagari a samar da tsaro da inganta rayuwar a kori fatara da talauci matasa su sami aikin yi a tabbatar da tsaro na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasa baki ɗaya.

Alhaji Ibrahim Al-amin Little ya ƙara jaddada kira ga al’ummar jihar Kano su fito su karɓi rijistar zaɓe don fatattakar gwamnatin zalunci da rashin tsaro yunwa da fatara da talauci.

  • Related Posts

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Sakamakon irin dimbin alheri da gudummawar da dan takarar majalisar tarayya na PDP, Hon. Alhaji Abubakar Ibrahim Maina, ke bai wa al’ummar karamar hukumar Tarauni, al’ummar…

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Baffa Babba Ɗan’agundi Ya Ɗauki Nauyin Horas Da Matasa 156 Sana’o’in Dogaro Da Kai

    Baffa Babba Ɗan’agundi Ya Ɗauki Nauyin Horas Da Matasa 156 Sana’o’in Dogaro Da Kai

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano