Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana cewa ƙananan hukumomi jihar Zamfara 14 za su baje kolin albarkatun da Allah ya hore musu a bukin baje koli na duniya karo na 46 da aka buɗe a jihar Kano.
Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu da Yawon Buɗe Ido na jihar Zamfara, Hon. AbdulRahman Tunbido Kogunan Maru ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin buɗe baje kolin a Kano .
Ya ƙara da cewa za su nuna kayan albarkatunsu ne domin duniya ta ga irin albarkatun da suke da su musamman a rana ta musamman da za a yi na jihar Zamfara a baje kolin na duniya na jihar Kano.
Ya nuna mutuƙar gamsuwa da shirin da aka yi na baje kolin da aka buɗe karo na 46 Kano ya ce ana samun kyautatuwarsa domin dama komai ana tafiya ne ana daɗa ingantawa, inda aka ga gyara a yi a cigaba, amma gaskiya sun yi abin a yaba suna burin a ce kowace jiha a Arewa ta shirya irin wannan domin al’umma su san me suke da shi na albarkatu da me suke ba da gudunmawa ta fannin bunƙasa kasuwanci.
Hon. AbdulRahman ya ce lokacin da suka zo gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Dakta Alhaji Dauda Lawan sun sami kasuwanci ya durƙushe bisa umurnin Gwamna don ganin an haɓaka kasuwanci suka duba masu ƙananan sana’o’i da suke buƙatar tallafi na sana’a ƙasa irin masu tuyar ƙosai, awara, masa da sauransu suka soma ba su tallafi na ₦50,000 kowane mutum da mutane 25,000 suka amfana.
Ya ƙara da cewa sun sake ba da wani tallafin ga ‘yan kasuwa ƙanana da matsakaita da manya da ƙananan ‘yan kasuwa an ba su tallafi na ₦150,000 kowanne su 2000 aka bai wa matsakaita ₦500,000 kowanne mutum 1000 su ma manyan ‘yan kasuwa aka ba kowanne ₦5,000,000 mutum 60 suka amfana a jimilla sun ba da tallafi na Naira biliyan ɗaya da Naira miliyan 100 a cikin watanni uku da suka wuce.
Hon. Abdulrahman Tunbido Kogunan Maru ya ce, akwai abubuwa da dama suna nan zuwa domin suna shirin haɗin gwiwa da bankin masana’antu domin samar da bashi mai sauƙi ga ‘yan kasuwa domin inganta masana’antunsu da kamfanoni.






