Daga Khalid Idris Doya
Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa bayan ya rasu bai amince ba, kuma bai yarda a ware rana ta musamman a ranar 2 ga watan Al-Muharram domin a riƙa yin Mauludin tunawa da ranar haihuwarsa ba.
Marigayin ya bayyana haka ne a cikin wasiyyar da bayar, cikin tawali’u da ƙanƙan da kai ya ce shi bai kai wanda za a riƙa gudanar da Maulidin tunawa da shi ba kamar yadda ake yi wa Manzon Rahama, irin su Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim Inyass.
Marigayi wanda ya rasu a ranar Alhamis 27/12/2025, ya bayyana cewa shi kawai Muƙaddami ne daga cikin Muƙaddaman Ɗariƙar Tijjaniyya, kuma hadimin Shehu Ibrahim Inyass, sannan surukinsa, inda ya bayyana cewa hakan ma kawai ya ishe abin alfahari.
Shehu Ɗahiru Bauchi ya nuna cewa idan har an ce kowane Muƙaddami za a ke masa Maulidin tunawa da shi, to kowane rana ma zai zama ana gudanar da maulidodi ne domin yawan Muƙaddaman da ake da su.
Ya bayyana da bakinsa cewa: “Amma ni ban yarda a ce wata rana za a yi taro yau 2 ga watan Muharram, ranar da aka haifi Shehu Ɗahiru muke yin Maulidi ban yarda ba. Kada a yi min bayan rayuwata.
“Amma na ji wani yana cewa Rabi’ul Auwal ya ƙunso mana (ya zo mana) da Annabi Muhammadu (SAW), Safar ya ƙunso mana Shehu Tijjani (R), Rajab ya ƙunso mana Shehu Ibrahim (R). Ya ce, wai Muharram ya ƙunso musu Shehu Ɗahiru! To wannan kada a sake faɗa, kada na sake ji.
“Ni ba kowa ba ne cikin wannan tsarin ni Muƙaddami ne. Ni Muƙaddami ne daga cikin muƙaddaman Shehu. Yanzu kowani Muƙaddamin Shehu sai an masa Maulidi ranar haihuwarsa nawa ke nan? Akwai ranar da za ta wuce ba a samu Maulidi ba?
“In an ce kowane Muƙaddamin Shehu za a masa Maulidi akwai ranar da ba Maulidi ke nan a Nijeriya? To ban yarda kada a sa sunana a cikin waɗanda ake wa wannan abu,” in ji shi.
Ya sake fayyace wasiyyar tasa da cewa, “Kuma ko na mutu kada a ce yau ranar 2 ga watan Muharram za a yi Maulidin Shehu Ɗahiru, ban yarda ba, ban yarda ba; A bar ni kamar sauran ‘yan’uwana Mukaddamai.”
Ya sake nanata cewa: “Ni ba kowa ba ne illa Muƙaddami cikin Muƙaddamin Shehu, kuma wannan ya ishe ni alfahari, hadiminsa, kuma surukinsa, Alhamdillahi.”
A gefe guda ya ce Maulidin tunawa da Shehu Ibrahim da ake yi a watan Rajab shi ne ya fara gudanar da shi.







