Za Mu Ci Gaba da Ba da Gudummawa Wajen Bunkasa Cigaban Al’ummar Gwagwarwa, Kano

– Barista Ibrahim Aliyu

Wannan rana ta farin ciki ce ga al’ummar garin Gwagwarwa, biyo bayan naɗin sabbin masu sarauta da Mai Girma Dagacin Gwagwarwa, Alhaji Usman Sanusi Aliyu, ya yi.

Wannan mataki na daga cikin abubuwan da ake sa ran zai ƙara haɗin kai da kuma ɗaukaka martabar masarautar Gwagwarwa, wadda ke da tsohon tarihi mai albarka.

Sabon Matawallen Gwagwarwa, Batista Ibrahim Isah Aliyu, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ’yan jarida bayan kammala bikin naɗin da aka yi masa.

Ya bayyana cewa, tun kafin wannan naɗin, yana daga cikin mambobin ƙungiyar raya garin Gwagwarwa, inda suke yin iya ƙoƙarinsu wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasar al’umma a ƙarƙashin ƙungiyar.

Matawallen ya kuma yi nuni da cewa, kamar yadda aka sani, Gwagwarwa na ɗaya daga cikin wuraren da suka tattaro ƙabilu daban-daban daga sassan ƙasar nan, kuma duk da haka ana rayuwa cikin zaman lafiya, ana auratayya, tare da zama tamkar ’yan’uwa.

A ƙarshe, Batista Ibrahim Isah Aliyu Matawallen Gwagwarwa ya miƙa godiyarsa ga Dagacin Gwagwarwa, Alhaji Usman Sanusi Aliyu, bisa wannan karamci da ya nuna na naɗa su muƙamai a masarautar.

Ya tabbatar da cewa za su kasance masu biyayya, tare da ba da gudunmawa wajen bunƙasa cigaba da ci gaban yankin Gwagwarwa baki ɗaya.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo