Mun Naɗa Sarautu 65 Domin Ƙarfafa Masu Ba Ga Gudunmawa Ga Cigaban Al’ummar Gwagwarwa –Dagaci

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Dagacin garin Gwagwarwa da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Kano, Alhaji Usman Sanusi Aliyu, ya bayyana cewa masarautar Gwagwarwa ta naɗa mutane 65 a muƙamai daban-daban tare da karrama wasu fitattun ‘ya’yan al’umma, domin ƙarfafa musu gwiwa kan gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne a makon da ya gabata yayin ganawarsa da manema labarai, jim kaɗan bayan kammala bikin naɗe-naɗen sarautu da karramawa da aka gudanar a garin Gwagwarwa.

Alhaji Usman Sanusi Aliyu ya ce, mutanen da aka naɗa da kuma waɗanda aka karrama sun fito ne daga kabilu da al’ummomi daban-daban, ba tare da nuna wariya ko bambanci ba, inda ya jaddada cewa masarautar Gwagwarwa ta ginu ne bisa tushen zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna.

“Mun zaɓi mutanen da suka cancanta ne, waɗanda ke taimaka wa talakawa kuma ke ba da gudunmawa ta zahiri wajen bunƙasa cigaban Gwagwarwa. Saboda haka, abin da ya fi dacewa shi ne mu ƙarfafa musu gwiwa ta hanyar jawo su a jiki da ba su mukamai,” in ji Dagacin.

Ya ƙara da cewa duk wanda ya ga waɗanda aka naɗa, zai tabbatar da cewa mutane ne nagartattu, masu kamala da kishin cigaban al’umma, ba wai Gwagwarwa kaɗai ba, har da ƙaramar hukumar Nasarawa, Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Dagacin ya kuma bayyana cewa nasarorin da ake samu a yankin sun samo asali ne daga zaman lafiya da haɗin kai da ke tsakanin al’ummar yankin, inda ya ce ba su yarda da fitina ba, kuma duk inda ta taso sukan yi ƙoƙarin kawar da ita domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Ya ce, kasancewar ƙaramar hukumar Nasarawa da garin Gwagwarwa na ɗauke da mutane masu harsuna da al’adu daban-daban, hakan bai hana su zaman lafiya da haɗin kai ba, domin suna zaune cikin fahimta da girmama juna.

Alhaji Usman Sanusi Aliyu ya ce tun kafin naɗa shi Dagaci, ya taɓa zama a Abuja inda ya yi karatu, lamarin da ya ba shi damar cuɗanya da ƙabilu da al’ummomi daban-daban, wanda hakan ya ƙara masa fahimtar muhimmancin haɗin kai da mutunta juna.

Ya jaddada cewa kafin gudanar da naɗe-naɗen sarautun, an yi cikakken shawarwari da majalisar masarautar Gwagwarwa, inda aka zaɓo mutane daga kabilu daban-daban kamar Ibira, Igala, Yarbawa, Igbo da sauran su, domin tabbatar da cewa kowa yana da wakilci kuma yana bada gudummawa wajen tafiyar da harkokin garin.

A ƙarshe, Dagacin ya nuna godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki, tare da jinjina ga Masarautar Kano, bisa irin kira da Mai Martaba Sarkin Kano ke yi na zaman lafiya da biyayya ga doka.

Ya ce al’ummar Gwagwarwa na alfahari da kasancewa ƙarƙashin Masarautar Kano, tare da jaddada biyayya ga umurnin Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum