Mun Taso Tare Tun Muna Yara” -Alhaji Ahmad Ali MTown kan Sabon Durɓin Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Alhaji Ahmad Ali Mai Gari, mallakin katafaren otel ɗin MTown and Suites da ke Dutse jihar Jigawa, ya bayyana farin cikinsa kan naɗin Alhaji Abdulƙadir Koguna a matsayin sabon Durɓin Kano, inda ya ce sun taso tare tun suna yara kuma sun shafe shekaru masu yawa suna abota ta ƙut-da-ƙut.

Alhaji Ahmad Ali ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida bayan masarautar Kano ta naɗa Alhaji Abdulƙadir Koguna a sabon muƙamin sarauta.

Ya ce sun haɗu tun daga makarantar Sakandare ta St. Thomas, inda suka fara karatu tare tun daga aji ɗaya a shekarar 1983.
“Ni da Durɓin Kano Alhaji Abdulƙadir Koguna aminai ne na kusa tun muna yara. Tun wancan lokaci na san shi da kyawawan halaye, karamci da son jama’a,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa naɗin da aka yi wa abokinsa ya zo a kan gaɓa, domin tun suna ƙanana yana nuna sha’awar harkar sarauta, yana da kyakkyawar tarbiyya da kishi ga al’umma.

Alhaji Ahmad Ali ya kuma bayyana cewa duk da kasancewarsa a Legas tsawon lokaci, suna tare da sabon Durɓin Kano a can, inda suke kula da harkokin kamfanonin mahaifinsu marigayi, tare da hulɗa da jama’a daban-daban.

Ya ce yawan jama’ar da suka halarci bikin naɗin, ciki har da ƙabilu daban-daban kamar Yarbawa, Ibo da sauran al’ummomi, na nuna cewa Alhaji Abdulƙadir Koguna mutum ne na kowa, mai haɗa kan jama’a ba tare da bambanci ba.

A cewarsa, “Allah ya yi Durɓin Kano Alhaji Abdulƙadir Koguna da zuciyar taimako. Ba wai arziƙi kaɗai yake da shi ba, har ma da son bayarwa da taimakon al’umma.”

Alhaji Ahmad Ali ya kuma jinjina wa Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi, kan yadda ya yi wannan naɗi, inda ya ce Sarkin da sabon Durɓin Kano sun daɗe suna tare tun lokacin da Sarkin ya kasance Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, kuma akwai kyakkyawar alaƙar biyayya, girmamawa da karamci a tsakaninsu.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo