Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Hon. Nasir Hassan Koguna, Galadiman Durɓin Kano kuma ƙani ga marigayi Durɓin Kano, ya bayyana sabon Durɓin Kano Alhaji Abdulƙadir Koguna a matsayin mutum mai haƙuri, karamci, tausayi da girmama jama’a, inda ya ce babu wanda ya fi shi sanin halayyarsa saboda sun taso tare tun suna yara.
Hon. Nasir Hassan Koguna ya bayyana hakan ne yayin da yake nuna godiyarsa ga masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi, bisa dawo da sarautar Durɓin Kano gida, lamarin da ya ce babban abin alfahari ne ga iyalan Kogunawa da Makoda baki ɗaya.
Ya ce marigayi Durɓin Kano ya shahara wajen kyautatawa jama’a ba kawai a Kano ba, har ma da Arewa da ƙasar nan baki ɗaya, inda ya bayar da gagarumar gudunmawa ga masarauta, jihar Kano da al’umma gaba ɗaya.
Saboda haka, ya ce suna yi wa sabon Durɓin Kano addu’a Allah ya ba shi ikon kwatanta, ko ma ya ɗara irin ayyukan alheri, adalci da kula da jama’a da marigayi ya yi.
Hon. Nasir ya ƙara da cewa, “Ni na fi kowa sanin halayyar Alhaji Abdulƙadir Koguna, domin tare muka taso; daki ɗaya, gado ɗaya, makaranta ɗaya, kamar ‘yan biyu muke. Mutum ne mai kyakkyawan hali, haƙuri da son jama’a, kuma jama’a shaida ne kan haka.”
Ya ce taron jama’a daga sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da ƙabilu da ba Hausawa ba da suka zo daga Legas da sauran yankuna domin taya su murna, hujja ce ta cewa sabon Durɓin Kano mutum ne na kowa.
A nata ɓangaren, Hajiya Rabi Koguna, ƙanwar sabon Durbin Kano, ta ce ba ta da abin cewa face godiya ga Allah bisa wannan naɗi, tare da yin addu’a ga mahaifinsu marigayi Durɓin Kano Allah ya jaddada rahama a gare shi.
Ta ce suna roƙon Allah Ya kama hannun sabon Durɓin Kano, Ya ba shi ikon riƙe iyali da jama’a kamar yadda mahaifinsu ya yi.
Ta bayyana cewa marigayi mahaifinsu ya dinga yi musu nasiha kan muhimmancin haɗin kai, kula da jama’a da kuma kada su manta da ƙauye, al’adar da ta ce sabon Durɓin Kano ya riga ya saba da ita tun yana yaro.
Hajiya Rabi ta ƙara da cewa Alhaji Abdulƙadir Koguna mutum ne mai tausayi da alheri, wanda idan ya yi maka abu ba ya son a yaɗa shi, kamar yadda mahaifinsu marigayi Durɓin Kano ya kasance.
Ta kuma gode wa Sarkin Kano Muhammad Sanusi bisa wannan karramawa da ya yi musu, inda ta ce naɗin ya zo ne a matsayin girmamawa ga marigayi mahaifinsu.
Shi ma Abba Waziri Koguna, Wazirin Koguna da Makoɗa, ya nuna godiya ga Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi bisa dawo da sarautar Durɓin Kano gida, inda ya yi addu’a ga magabata marigayi Abdulƙadir Koguna da Muhammad Hassan Koguna Allah Ya gafarta musu, Ya kuma haɗa kan bayansu.
Abba Waziri Makoɗa ya ce suna da yaƙini cewa sabon Durɓin Kano Alhaji Abdulƙadir Lawan Koguna ya gaji kyawawan halaye daga magabatansa, kuma za su ci gaba da yi masa addu’a Allah Ya ba shi ikon haɗa kan al’umma da ci gaba da ayyukan alheri.







