Tun Kafin Naɗin Sarauta, Mahaifinmu Mutum Ne Mai Kyautata Wa Al’umma -Sani Abdulkadir Koguna

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Sani Abdulƙadir Koguna, ɗa ga sabon Durɓin Kano, Alhaji Abdulƙadir Koguna, ya bayyana farin cikinsa tare da miƙa godiya ga Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi, bisa naɗin sarautar da ya yi wa mahaifinsu.

Ya ce yawan jama’ar da suka halarci bikin naɗin daga sassa daban-daban ya sanya su cikin matuƙar farin ciki, yana mai jaddada cewa hakan wata alama ce ta yadda mahaifinsu ke zaman lafiya da kowa tare da kyakkyawar alaƙa da al’umma.

Sani Abdulƙadir Koguna ya ƙara da cewa suna da cikakken tabbaci mahaifinsu, a matsayinsa na Durɓin Kano, zai ci gaba da riƙe halayen karamci, mutumtaka da taimakon jama’a da gidansu ya daɗe yana yi, har ma ya ƙara zage dantse a kai.

Ya tunatar da cewa marigayi Durɓin Kano, Allah ya jiƙansa, an san shi da kyakkyawan hali, kyauta da tausayi ga al’umma, tare da ƙarfafa zumunci da kula da ’yan’uwa.

Ya ce duk waɗannan siffofi sun taso suna gani a mahaifinsu tun kafin a yi masa wannan naɗin, don haka naɗin sarautar tamkar “mayar da kwarya a gurbin ta” ne.

A ƙarshe, Sani Abdulkadir Koguna ya ce a madadin ’ya’yan gidan, suna yi wa mahaifinsu fatan alheri da addu’ar Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, tare da alƙawarin ba shi cikakken goyon baya, haɗin kai da biyayya domin kare mutuncin sarautar da aka ba shi.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani