’Yan’uwa sun nuna farin ciki da naɗin Barhama a matsayin Sarkin Zabarmawan Kano

Daga Ibrahim Muhammad Kano

’Yan’uwa da makusantan sabon Sarkin Zabarmawan Kano, sun bayyana matuƙar farin cikinsu da naɗin Alhaji Barhama Hussaini Yahaya a matsayin Sarkin Zabarmawa na farko a Jihar Kano.

Ɗaya daga cikin ’yan’uwan Sarkin, Alhaji Mustapha Abdulrazak, ya bayyana cewa suna matuƙar godiya ga Allah bisa wannan naɗi, inda ya ce Alhaji Barhama mutum ne mai karamci da kyawawan halaye, wanda ya cancanci wannan matsayi duba da irin gudunmawar da yake bayarwa ga al’umma.

Ya ce sabon Sarkin Zabarmawan Kano mutum ne mai kula da ’yan’uwa da dangi, mai tausayi da jin ƙan al’umma, halaye da aka shaida a kansa tsawon lokaci.

Alhaji Mustapha Abdulrazak ya ƙara da cewa a matsayinsu na ’yan’uwa, za su ci gaba da ba shi cikakken goyon baya domin kare martabar sarautar da aka ɗora masa, tare da yi masa fatan alheri a sabon muƙamin nasa.

Ya kuma gode wa mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi, bisa karamci da girmamawar da ya nuna wa Zabarmawa ta hanyar naɗa Alhaji Barhama a matsayin Sarkin Zabarmawa, inda ya ce hakan ya nuna ƙima da mutunta Zabarmawa da ke zaune tare da al’ummar Kano tun kaka da kakanni.

A nasa jawabin, ɗaya daga cikin shugabannin Zabarmawa da ya halarci bikin, Alhaji Muktar Mika’il Minna, shugaban Ƙungiyar Cigaban Zabarmawa ta Jihar Neja, kuma mataimakin shugaban Zabarmawa Development Association (ZAGA) na ƙasa, ya ce wannan naɗi ya nuna amincewa da nagartar sabon sarkin.

Ya ce babu abin da Zabarmawa za su ce face godiya ga Sarkin Kano da al’ummar Kano baki ɗaya bisa soyayya, yarda da kuma girmamawar da suka nuna musu.

Alhaji Muktar Mika’il Minna ya yi fatan al’ummar Zabarmawa za su bai wa Sarkin Zabarmawan Kano cikakken haɗin kai, goyon baya, shawarwari da addu’o’i, domin Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa yadda ya dace.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo