Daga Ibrahim Muhammad Kano
Masarautar Kano, a yammacin ranar Laraba 21 ga Janairu, 2026, ta naɗa Alhaji Barhama Hussaini Yahaya a matsayin Sarkin Zabarmawa na farko a Jihar Kano.
Mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi ne ya jagoranci bikin naɗin, wanda ya samu halartar ɗimbin jama’a daga sassa daban-daban na cikin gida da wajen ƙasar nan.
Taron naɗin ya haɗa sarakuna, shugabannin kungiyoyin Zabarmawa daga jihohin Nijeriya, da kuma baƙi daga ƙasashen Nijar, Togo, Mali, Ghana, tare da ’yan kasuwa, manyan ma’aikata da sauran al’umma daga wurare daban-daban na duniya.
Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi, ya bayyana cewa an yi la’akari da kyawawan halaye, taimako ga al’umma, jajircewa wajen cigaban addini, haɗin kan jama’a da kuma rawar da yake takawa wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin Zabarmawa da al’ummar Kano da Arewa baki ɗaya, kafin naɗa Alhaji Barhama Hussaini Yahaya a wannan mukami.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala bikin naɗin, sabon Sarkin Zabarmawan Kano, Alhaji Barhama Hussaini Yahaya, ya nuna matuƙar godiyarsa ga mai martaba Sarkin Kano bisa wannan karramawa, wadda ya ce ta shafi dukkan al’ummar Zabarmawa da ke Jihar Kano da Nijeriya gaba ɗaya.
Ya bayyana cewa al’ummar Zabarmawa sun daɗe suna zaman lafiya da al’ummar Kano tun kaka da kakanni, inda ya ce da dama daga cikinsu an haife su ne a Kano, kuma za su ci gaba da kiyaye mutunci, zaman lafiya da bayar da gudummawa wajen cigaban Jihar Kano.
Sarkin Zabarmawan Kano na farko ya kuma jaddada alƙawarinsa na yin biyayya ga Masarautar Kano da Gwamnatin Jihar Kano, tare da haɗa kan al’umma domin bunƙasa cigaban jihar.
A nasa ɓangaren, Alhaji Muhammadul Bakari, makusanci, kuma abokin sabon sarkin, ya bayyana farin cikinsa bisa yadda taron ya samu halartar jama’a masu yawa daga ciki da wajen ƙasar nan.
Ya ce haɗin kai da kyawawan halayen Sarkin Zabarmawa, Alhaji Barhama Hussaini Yahaya -wanda ya bayyana a matsayin mutum mai asali, haƙuri da son jama’a -sune manyan abubuwan da suka jawo wannan gagarumin taron jama’a.







