Kungiyar Izala Ta Raba Kayan Abinci Da Tufafi Ga Mabuƙata A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ƙungiyar Izalatul Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah (Izala) reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Imam Abdullahi Saleh Pakistan, ta gudanar da rabon tallafin kayan abinci da tufafi ga marayu, kamar yadda ta saba a ƙarshen watan Azumin Ramadan, a harabar Masallacin Tudun Murtala.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da rabon tallafin ga gidajen marayu sama da 1,000, mataimakin shugaban ƙungiyar, Sheikh Muhammad Ahmad Usman Bichi, wanda ya wakilci Farfesa Imam Abdullahi Saleh Pakistan, ya bayyana cewa an fara wannan shiri ne tun shekaru da dama da suka gabata, kuma har yanzu ana ci gaba da gudanar da shi cikin nasara, har wasu jihohi da ƙungiyoyi suka kwaikwaya.

Ya ce a kodayaushe Imam Abdullahi Saleh Pakistan yana jan hankali kan tsoron Allah da kuma taimakon marayu, yana mai cewa an fara wannan aiki ne da ƙaramin tsari, amma daga bisani ya bunƙasa har ya bazu zuwa wasu jihohi, inda ma wasu gwamnatoci ke shiga cikin shirin domin tallafawa marayu.

Sheikh Bichi ya ƙara da cewa yana da matuƙar muhimmanci a tallafawa marayu domin su ma su yi shagalin Sallah kamar sauran yara masu iyaye, ba tare da jin yunwa ko rashin sutura ba.

Ya jaddada cewa duk wani taimako da za a yi wa maraya, a yi shi ne don neman yardar Allah, wanda shi ne babban saƙon shugabannin ƙungiyar.

Haka kuma ya yi addu’ar Allah ya saka wa dukkanin mambobin kwamitin tallafin da masu bayar da gudunmawa da alheri, yana mai cewa sune ke wahala wajen tattara kayan tallafin da rabawa.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa ɗaukar marayu a matsayin ‘ya’yansu, su riƙa haɗa su da ‘ya’yansu wajen ci, sutura da makaranta, tare da ba su tarbiyya iri ɗaya.

Ya ce wannan haɗin kai shi ne zai ba su damar jin cewa ba su rasa kulawar uba ba.

A cewarsa, ware marayu a wuri guda kawai don karatu ba tare da cuɗanya da sauran yara ba, ba zai ba su cikakkiyar tarbiyya ba kamar yadda haɗuwa da ‘ya’yan gida ke yi.

A nasa ɓangaren, shugaban majalisar malamai na ƙungiyar Izala reshen jihar Kano, Malam Hussaini Yakub Rano, ya bayyana cewa marayu na da buƙatar kulawa a kowane lokaci, ba wai a watan Azumi kaɗai ba.

Ya bayar da misali da wasu marayu da aka gano suna rayuwa cikin tsananin talauci, har ma ba sa samun damar yin wanka yadda ya kamata saboda rashin kuɗin sayen ruwa.

Ya jaddada cewa ya kamata a riƙa taimakon marayu a duk shekara, ba tare da jiran watan Ramadan ba, yana mai cewa yin hakan da wuri kan taimaka musu wajen shawo kan wasu buƙatu na rayuwa kamar karatu da sauran hidimomi.

Haka zalika ya yi kira ga al’umma da kada su ɗauka cewa sai masu kuɗi ne kaɗai za su taimaka, yana mai tunatar da su Hadisin Manzon Allah (SAW) da ke cewa: “Ku kare kanku daga wuta ko da da rabin dabino ne.”

“Don haka, kada a raina kowane irin taimako, komai ƙanƙantarsa,” in ji shi.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake gujewa auren matan da ke da marayu, yana mai cewa hakan na jawo musu wahala da tauye musu haƙƙinsu na rayuwa.

Ya ce ya kamata maza su riƙa aurensu da kyakkyawar niyya domin kare mutuncinsu da na ‘ya’yansu, tare da samun lada mai yawa daga Allah.

A cewarsa, da yawa daga cikin iyayen marayu na rasa damar sake aure ne saboda suna da ‘ya’ya, alhali kuwa hakan bai kamata ya zama tarnaƙi ba.

Ya buƙaci a canza wannan ɗabi’a domin taimakawa al’umma.

A yayin ƙaddamar da rabon tallafin, sakataren kwamitin tattara tallafin, Malam Sani Jibrin, ya bayyana sunayen mutane da kamfanonin da suka bayar da gudunmawa, wanda hakan ya taimaka wajen samar da kayan da aka raba wa ɗimbin marayun da suka amfana.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength