Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ɗaya daga cikin jagororin Kwankwasiyya a jihar Kano, kuma tsohon mai magana da yawun jam’iyyar NNPP a jihar, Hon. Injiniya Ibrahim Ƙaraye, ya yi kira ga al’umma da su shiga jam’iyyar ADC domin ceto kasar nan daga matsalolin da ake ciki.
Injiniya Ibrahim, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Ƙaraye, ya bayyana hakan ne a lokacin bukukuwan Sallah da aka gudanar a gidan Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya ce siyasar ƙasar nan na dab da sauyawa, musamman ɓangaren adawa.
Ya ce duk mai bibiyar yadda al’amura ke tafiya zai fahimci hakan, lura da yadda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, wanda ya zo na uku a zaɓen 2023, ya halarci taron a Kano, sannan ya sake dawowa tare da shugabannin jam’iyyar ADC, ciki har da shugabanta David Mark, sanatoci da ‘yan majalisun tarayya, domin halartar wannan taro.
A cewarsa, al’umma na bin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ne saboda amincewar da suke da shi, inda ya ce idan Kwankwaso ya samu dama, jama’a ma za su amfana.
Ya ƙara da cewa idan aka duba tarihin siyasar Nijeriya tun daga 1999, babu wani babban ɗan siyasa da duk lokacin da ya sauya sheƙa daga jam’iyya mai mulki zuwa ta adawa yake samun karɓuwa kamar Kwankwaso.
“Yana yin hakan ne saboda talakawa da kuma ƙaunar al’umma, da nufin kawo sauyi. Duk lokacin da ƙasa ta shiga matsala, irin waɗannan shugabanni ne ke ƙoƙarin gyara al’amura,” in ji shi.
Ƙaraye, ya tuna cewa a shekarar 2014 sun bar jam’iyyar PDP suka koma APC, yana mai cewa yanzu ma suna shirin haɗaka a jam’iyyar ADC domin ceto al’umma daga halin ƙunci da wahalhalun rayuwa.
Ya kuma ce al’ummar jihar Kano sun daɗe suna goyon bayan Kwankwaso, tun daga shekarar 2007, inda ya ce bai taɓa tsayawa takara ko tsayar da ɗan takara ba tare da samun ƙuri’u ƙasa da miliyan ɗaya ba.
A cewarsa, shiga jam’iyyar ADC da suka yi zai ba ta sabon ƙarfi, yana mai cewa jam’iyyar ta daɗe tana nan, amma mutane da dama ba su san da ita ba.
“Daga yanzu, duk wanda ya lura zai ga cewa jam’iyyar ADC za ta samu karɓuwa sosai a faɗin ƙasar nan,” in ji shi.
Ya bayyana fatan cewa jam’iyyar za ta yi nasara a zaɓuɓɓukan 2027, tare da kira ga jama’a da su yi rijista da jam’iyyar, su kuma dage wajen yaƙi da zalunci domin ƙwato ‘yancin su.
“Dole ne a haɗa kai, a yi haƙuri, sannan za a samu canjin da ake nema,” in ji Ƙaraye.






