Daga Ibrahim Muhammad Kano
Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano, Alhaji Adam Salihu, wanda aka fi sani da Mai Gidan Gona na Garun Ali a Ƙaramar Hukumar Garko, ya bayyana cewa sun bi jagoransu Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da zuciya ɗaya zuwa jam’iyyar ADC domin tabbatar da nasararta a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya ce sun koma jam’iyyar ne bisa umarnin jagoransu, inda ya jaddada cewa za su gudanar da tafiyar cikin gaskiya tare da tabbatar da cewa al’ummar Kano da Nijeriya baki ɗaya sun ga tasirin wannan sabon mataki.
Mai Gidan Gona ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen taron komawar Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso jam’iyyar ADC da aka gudanar a harabar gidansa da ke kan titin Miller.
Ya ƙara da cewa ‘yan Kwankwasiyya na da ɗabi’ar bunƙasa duk wata jam’iyya da suka shiga, yana mai cewa ko da jam’iyyar ba ta da ƙarfi, suna iya ba ta rai ta hanyar tsari da aiki tuƙuru.
“Jam’iyyar ADC da muka shiga yanzu za ta bunƙasa sosai, domin mun shirya tsaf don yin aiki tuƙuru har sai mun ga an samu sauyin gwamnati daga sama har ƙasa da yardar Allah,” in ji shi.
Ya kuma kwatanta tsarin Kwankwasiyya da aikin soja, inda ya ce duk da cewa ana bin kwamanda, idan wani abu ya faru, ba yana nufin an gama yaƙi ba, domin a cikin tafiyar akwai mutane da dama da za su iya jagoranci.
A cewarsa, a Ƙaramar Hukumar Garko suna da gogaggun ‘yan siyasa da suka haɗa da Alhaji Sani Yariman Kwas da sauran masu ruwa da tsaki, waɗanda ke da ƙwarewa da mutunci wajen tafiyar da harkokin siyasa.
Ya ƙara da cewa ƙofarsu a buɗe take ga duk masu son shiga tafiyar, yana mai cewa suna da ƙarfin gwiwa cewa goyon bayan da suke samu yana ƙara haɓaka a yankin Garko.
Mai Gidan Gona ya bayyana cewa fatansu shi ne gwamnatin Kano da suka taimaka wajen kafawa ba za ta yi musu cin amanar da za ta tilasta su sake ɗaukar wani mataki ba.
Ya ce suna fatan a wannan sabon tsari da suke ciki, za a kauce wa maimaita irin abubuwan da suka faru a baya, yana mai jaddada cewa Kwankwaso shi ne madubin tafiyarsu a siyasa.
“Duk inda jagora ya ce mu shiga, za mu shiga da yardar Allah,” in ji shi.






