Daga Ibrahim Muhammad Kano
Tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Dala, Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala, ya bayyana cewa zaɓen sabbin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kano da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Hon. Umar Haruna Doguwa ya gudana yadda ya kamata.
Namadi Dala ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce zaɓen da aka gudanar zai ƙara ƙarfafa haɗin kai da bunƙasa cigaban jam’iyyar a Jihar Kano.
Ya taya sabbin shugabannin jam’iyyar da aka zaɓa murna tun daga matakin mazabu, ƙananan hukumomi har zuwa matakin jiha, bisa yadda aka gudanar da zaɓen cikin fahimtar juna, haɗin kai da kuma kwanciyar hankali.
A cewarsa, yadda aka gudanar da zaɓen cikin gamsuwa da amincewar kowa alama ce da ke nuna cewa jam’iyyar APC za ta samu gagarumar nasara a zaɓe mai zuwa na shekarar 2027, musamman idan aka yi la’akari da cewa Jihar Kano cibiyar siyasa ce a Najeriya.
Namadi Dala ya kuma gode wa manyan jagororin jam’iyyar APC a Kano bisa haɗin kai da suka nuna domin tabbatar da nasarar zaɓen.
Ya ambaci Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma Sanatan Kano ta Arewa kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, bisa rawar da suka taka wajen haɗa kan jam’iyyar.
Ya ce shigowar Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC wata kyakkyawar manufa ce ta cigaban Jihar Kano, domin a cewarsa gwamnan mutum ne mai ƙwazo da jajircewa wajen kawo cigaba ga al’ummar jihar.
Namadi Dala ya kuma bayyana cewa sauran jagororin jam’iyyar da suka haɗa da Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Barau I. Jibrin sun yi alkawarin ci gaba da haɗa kai da Gwamna Abba Kabir Yusuf domin bunƙasa cigaban Jihar Kano da al’ummarta.
Dangane da sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa, Namadi Dala ya ce mutum ne mai jajircewa da aiki tuƙuru, yana mai cewa ya yi imanin cewa zai jagoranci jam’iyyar yadda ya kamata domin samun nasara a zaɓe mai zuwa.
Ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da su bai wa shugabanninsu goyon baya a kowane mataki domin tafiya tare cikin haɗin kai.
A ƙarshe, Namadi Dala ya bayyana fatan cewa idan aka zo matakin fitar da ’yan takara, za a yi hakan cikin fahimtar juna da kwanciyar hankali, tare da bai wa duk wanda ya samu nasara cikakken goyon baya domin samun nasara a zaɓe.
Ya ƙara da cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a dukkan matakai, daga ’yan majalisun jiha da na tarayya, sanatoci da gwamnoni, tare da tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027.






