Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana cewa mata na ƙoƙari sosai wajen ƙirƙirar harkokin kasuwanci, sai dai da dama ba sa samun damar bunƙasa harkokinsu yadda ya kamata sakamakon rashin hanyoyin samun jari.
Samira Saleh, babbar sakatariyar ɓangaren mata ta Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Ƙasa (NACCIMA), ce ta bayyana hakan yayin da take zantawa da ‘yan jarida a taron ƙwatan shekara na cibiyoyin kasuwanci na ƙasa da aka gudanar a Kano.
Ta bayyana taron a matsayin mai muhimmanci, inda ta ce mahalarta sun zo daga jihohi daban-daban na ƙasar nan domin ganin irin ayyukan da Gwamnatin Kano ke yi, da kuma fahimtar damar da ake da su a fannonin kasuwanci.
Ta ƙara da cewa kasuwanci a Kano na da inganci matuƙa, inda akwai damammaki iri-iri da mutane za su iya shiga, tun daga ƙananan kasuwanci na talla a kan titi, zuwa manyan harkokin masana’antu na sarrafa kayayyaki.
Ta ce Kano ta zama wata muhimmiyar cibiyar kasuwanci da ke samar da ayyukan yi ga matasa, maza da mata.
Samira Saleh ta ce mata na taka rawa sosai a harkar kasuwanci, sai dai duk da haka damar da suke samu ba ta kai ta maza ba.
Ta ce a matsayinsu na shugabanni a ɓangaren mata na NACCIMA, za su ci gaba da wayar da kan mata kan hanyoyin da suka dace domin samun damar jari da bunƙasa kasuwancinsu.
Ta kuma bayyana cewa akwai hanyoyi da dama da mata za su iya samun tallafin jari, musamman ta bankuna, amma rashin sani da tsari na hana su cin gajiyar waɗannan damammaki.
Ta ce mata da dama sun fara kasuwanci, amma idan aka tambaye su ƙalubalen da suke fuskanta, galibi suna ambaton rashin damar samun rance daga bankuna.
A ƙarshe, ta ce za su mayar da hankali wajen wayar da kan mata kan yadda za su bunƙasa kasuwancinsu, musamman ta hanyar koyar da su yadda za su nemi rance a bankuna.
Ta kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su taimaka wajen faɗakar da mata su shiga su yi rijista da cibiyoyin kasuwanci da masana’antu a jihohinsu, domin hakan zai ba su damar samun goyon baya da bunƙasa harkokinsu.







