Zamantakewa Tsakanin Ma’aurata Na Ɗorewa Ne Da Yin Haƙuri Da Juna -Injiniya Bashir

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana aure a matsayin al’amari na zaman haƙuri, inda dole ne ma’aurata su fahimci cewa akwai lokutan da rashin jituwa kan iya tasowa, amma a yi aiki da koyarwar Manzon Allah (SAW) wajen magance matsaloli.

Injiniya Bashir ne ya bayyana hakan bayan ɗaurin auren ɗansa, Sadik Bashir, da A’isha Farfesa Tijjani Hassan Darma, wanda aka gudanar a harabar Masallacin Juma’a na tsohuwar Jami’ar Bayero, a ranar Asabar.

Ya yi nuni da cewa mutuntawa ita ce ginshiƙin zamantakewar aure, yana mai jaddada cewa bai kamata a riƙa zagi a tsakanin ma’aurata ba, domin hakan na iya janyo rashin jituwa.

Ya ce idan miji ya saba zagin matarsa, wata rana za ta iya ramawa, wanda hakan zai ƙara tsananta matsalar.

Ya ƙara da cewa ya kamata a riƙa ɗaukar matakai kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar, na kaucewa mace idan ta aikata abin da ya ɓata rai, ba tare da duka ko zagi ba.

Ya ce hakan na sa mace ta yi nadama, sannan idan aka dawo sai a zauna a tattauna domin fahimtar juna da sulhu.

Injiniya Bashir ya jaddada cewa ɗorewar zamantakewar aure na samuwa ne ta hanyar haƙuri da juna, inda ya ce dole ne a rayuwa a samu lokutan farin ciki da kuma akasin haka.

Haka kuma, ya nuna damuwa kan yawaitar saki da ake samu a tsakanin ma’aurata, yana danganta hakan da sakacin iyaye, musamman a Arewacin Nijeriya, wajen tarbiyantar da ’ya’yansu kan yadda ake gudanar da zamantakewar aure.

Ya ce ya kamata iyaye su riƙa zama da ’ya’yansu su koya musu yadda za su tafiyar da rayuwar aure cikin hikima.

A ƙarshe, uban Angon ya nuna matuƙar farin ciki tare da godiya ga mutanen da suka halarci bikin aure daga wurare daban-daban, duk da tsadar sufuri da ake ciki.

Ya ce baya ga mutanen Kano, akwai waɗanda suka zo daga Katsina da garin Okene da sauran sassan ƙasar nan.

Haka kuma ya gode wa abokan aikinsa da shugabanninsu daga Jami’ar Maryam Abacha (MAUN) bisa zumuncin da suka nuna masa.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo