Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta saki wasu jami’an gwamnatin jihar Kano da ake zargi da hannu a wata taƙaddama ta siyasa, bayan sun shafe kusan awanni huɗu a hedikwatarta domin amsa tambayoyi.
Jami’an da aka bayar da belinsu sun haɗa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, da Salisu Yahaya Hotoro, tare da Ibrahim Adam.
Rahotanni sun ce an sake su ne bayan sun cika wasu sharuɗɗan beli da hukumar ta gindaya.
Majiyoyi sun bayyana cewa ƙungiyar Kwankwasiyya Movement ce ta shigar da ƙorafi a kansu, inda ta zarge su da kalaman da ake ganin sun ɓata suna da kuma tayar da kura a fagen siyasa.
Hakan ne ya sa Hukumar DSS ta gayyace su domin gudanar da cikakken bincike.
Binciken na DSS ya mayar da hankali ne kan zarge-zargen da suka shafi al’amuran siyasa, musamman zargin ɓata suna ga jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, da tsohon mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, da kuma Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufa’i Sani Hanga, tare da sauran mambobin ƙungiyar.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga ɓangarorin da ake zargi ko kuma jagororin Kwankwasiyya dangane da lamarin.
Sai dai masana harkokin siyasa na ganin cewa irin wannan taƙaddama na iya ƙara zafafa yanayin siyasar jihar Kano, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a harkokin siyasa.
Ana sa ran Hukumar DSS za ta ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin, tare da ɗaukar matakin da ya dace bisa sakamakon binciken.






