Me Ya Hana Gwamnonin Kano Da Katsina Halartar Taron Tunawa Da Malam Aminu Kano Karo Na 43?

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An gudanar da taro karo na 43 domin tunawa da marigayi Malam Aminu Kano, wanda Cibiyar Nazarin Dimokuraɗiyya ta Jami’ar Bayero da ke Kano ta shirya, a ranar Juma’a, a babban ɗakin taro na cibiyar da ke gidan Mambayya.

Taron na bana, wanda tsohon Hafsan Hafsoshin ƙasar nan mai ritaya, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya jagoranta, ya samu halartar tsohon Babban Kwanturola na Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa mai ritaya, Muhammad Babandede, da tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, tare da wasu jami’an tsaro da ragowar tsofaffin ’yan NEPU.

Farfesa Nazifi Abdullahi Darma, tsohon Kwamishina na ƙungiyar ECOWAS, wanda ya gabatar da muƙala, ya ce ƙungiyar ECOWAS za ta ci gaba da kasancewa mai tasiri ne idan ta ɗauki matakan da za su haɗa kan jama’a ta fuskar tattalin arziƙi da tsaro.

Ya ce matsalolin tsaro na da alaƙa da ci gaban tattalin arziƙi da rayuwar al’umma, domin idan babu zaman lafiya, babu yadda za a fita sana’a, noma ko ciniki, kuma babu wanda zai zuba jari a ƙasa.

Ya ƙara da cewa idan akwai rashin zaman lafiya a ƙasa ɗaya, dole ne sauran ƙasashe su haɗa kai domin magance matsalar, domin gazawa na iya sa matsalar ta yaɗu zuwa wasu ƙasashe.

Ya ba da misali da cewa tun kusan shekaru 300 da suka gabata, kafin zuwan Turawa, akwai cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka ta Yamma. Saboda haka idan wata matsala ta shafi wata ƙasa, wajibi ne a haɗa kai a magance ta kafin ta shafi kowa.

Da yake magana a kan maƙasudin taron, Daraktan Cibiyar Nazarin Dimokuraɗiyya ta Malam Aminu Kano, Farfesa Habu Muhammad Fagge, ya bayyana cewa an samu matsaloli da dama a yankin Afirka ta Yamma, ciki har da yawaitar juyin mulki da shigowar ’yan ta’adda.

Ya ce idan kana cikin gidanka kana lafiya, amma maƙwabtanka ba sa cikin zaman lafiya, hakan yana nufin kai ma ba ka cikin cikakken tsaro. “Saboda haka ne aka shirya tattauna wannan matsala domin galibin ƙasashen da ke kewaye da Nijeriya ba Ingilishi suke magana ba, Faransanci suke yi sakamakon mulkin mallakar Faransa,” in ji shi.

Ya yi nuni da cewa ta waɗannan ƙasashe ne makamai ke shigowa, kuma idan wata ƙasa daga cikinsu ta samu matsalar rashin zaman lafiya, to hakan na iya shafar sauran. Saboda haka ne aka shirya wannan taron lakca domin a samo mafita daga cikinmu.

Farfesa Habu Muhammad Fagge ya gode wa shugaban taron, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, bisa halartar taron da kuma ɗaukar nauyin duba marasa lafiya tare da ba su magani kyauta a daidai lokacin da taron ke gudana, ƙarƙashin gidauniyarsa.

Ya ce wannan ya yi daidai da irin manufofin marigayi Malam Aminu Kano lokacin da yake Ministan Lafiya a gwamnatin mulkin soja ta Yakubu Gowon, inda ya gabatar da tsarin lafiya ga kowa.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Farfesa Aliyu Mu’azu, wanda ya wakilci Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana cewa Jami’ar Bayero a shirye take ta ƙara ba da dukkan gudunmawar da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da irin wannan taro.

A jawabinsa, Muhammad Babandede, tsohon kwanturola na Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa, ya ce lokaci ya yi da ’yan siyasa za su riƙa halartar irin wannan taro domin ɗaukar darasi daga rayuwar Malam Aminu Kano.

Ya ja hankalin shugabanni, musamman ’yan siyasa na Arewa, da cewa bai kamata su riƙa ƙauracewa irin wannan muhimmin taro ba, musamman gwamnonin jihohi, domin hakan babban kuskure ne.

Babandede ya ce taron bana ba wai na biki kawai ba ne, illa na yin koyi da halayen Malam Aminu Kano.

Ya ce hatta talakawa ya kamata su yi koyi da rayuwarsa, domin a zamaninsa talakawa ne ma suke bayar da kuɗin mota domin tafiya taro, kuma shugabanni ba sa cin amanarsu.

Shi ma a nasa tsokacin, tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya yi kira da a ba tarihi muhimmanci tare da koyar da shi a makarantu saboda amfaninsa ga rayuwar al’umma.

Ya bayyana cewa shi ma ya karanci tarihi a digirinsa na farko da na biyu, don haka kiyaye tarihi da yin koyi da ayyukan alheri irin na marigayi Malam Aminu Kano yana da matuƙar muhimmanci wajen haɗin kai da ci gaban ƙasa.

Burutai ya ja hankalin mutane kan muhimmancin zaman lafiya da kuma zaɓen shugabanni nagari, tare da amfani da ƙuri’arsu wajen kawar da duk wanda bai kyautata musu ba a lokacin zaɓe.

Shi ma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar, ya nuna takaicinsa kan rashin halartar taron da aka gayyaci gwamnonin Kano da Katsina, amma ba wanda ya halarta ko ya turo wakili. Haka kuma babu wani ɗan majalisar tarayya ko na jiha, ko sanata da ya halarci wannan muhimmin taro.

Farfesa Hafizu ya yi nuni da cewa batun Malam Aminu Kano bai tsaya ga siyasa kaɗai ba, ya haɗa har da koyarwar addini, domin har makarantar Islamiyya shi ne ya fara ƙirƙiro ta a Kano. Saboda haka, ya ce abin takaici ne yadda wasu ’yan siyasa ba sa ba irin wannan taro muhimmanci.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum