Ni ‘Yar Jam’iyyar PDP Ce, Ba Ni Da Niyyar Fita Daga Cikinta -Amb. Zainab Audu Bako

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Jigo a jam’iyyar PDP ta ƙasa daga jihar Kano, Ambasada Hajiya Zainab Audu Bako, ta musanta raɗe-raɗin da ake yi cewa tana shirin ficewa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC.

Zainab Audu Baƙo, wadda ta taɓa riƙe muƙamin shugabar mata ta jam’iyyar PDP a shiyyar Arewa maso Yamma, ta tabbatar wa wakilinmu cewa:
“Ba gaskiya ba ne, ni ‘yar PDP ce, ba ni da niyyar fita daga cikinta.”

Wannan raɗe-raɗi ya taso ne bayan ficewar ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar a Kano, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, wanda ake kyautata zaton zai koma jam’iyyar APC.

Hajiya Zainab Audu Baƙo ta ce tana nan daram a jam’iyyar PDP, sannan ta yi kira ga al’ummar ƙasar nan, musamman matasa maza da mata, da su je su yi rajista da jam’iyyar PDP, wadda suke fatan za ta yi nasara a zaɓe mai zuwa domin kyautata al’amuran ci gaban ƙasar nan.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum