Hon. Kabiru Haruna Wakili: Fatan Al’ummar Fagge A Majalisar Tarayya 2027 Ya Amsa Kiransu

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Al’ummar ƙaramar hukumar Fagge na yabawa da irin ƙoƙari, kishin cigaban jama’a da kuma taimakon da ɗaya daga cikin matasan yankin ke bayarwa a fannoni daban-daban na rayuwa, duk da cewa ba ya riƙe da wani muƙami na siyasa a halin yanzu.

Hon. Kabiru Haruna Wakili ya yi fice a Fagge wajen hidimtawa al’umma. Shi ɗan siyasa ne da ke gina ci gaban matasa tun daga tushe, ta hanyar ba su tallafin sana’o’in dogaro da kai da kuma tallafa musu wajen neman ilimi.

Saboda kishin da yake da shi na ganin ya ci gaba da tallafa wa jama’a, al’ummar Fagge ke nuna masa goyon baya a tafiyarsa ta siyasa. Suna da yaƙinin cewa idan ya samu dama, zai ƙara bunƙasa yankin.

Wakili ya shahara a fagen gwagwarmayar siyasa. Ya tsaya da ƙafarsa, ya taɓa jagorantar wata jam’iyya, sannan ya yi fafutukar tsayawa takarar Majalisar Tarayya a zaɓen da ya gabata.

A yanzu, Hon. Kabiru Haruna Wakili ɗan jam’iyyar APC ne. Yana da kyakkyawar alaƙa da mutuntaka a tsakanin ‘yan siyasa da sauran al’umma a Fagge tun daga tushe. Wannan ne ya sa, yayin da ake tunkarar zaɓukan 2027, mutane ke ganin ya kamata a mara masa baya.

Matasa da manya, maza da mata a Fagge na jan hankalin masu haƙƙin zaɓen fitar da gwani a APC da su tsayar da mutane masu nagarta da ke tare da al’umma. Suna da kyakkyawan fata ga Hon. Wakili a wannan kakar zaɓe.

Al’ummar Fagge sun ce Hon. Kabiru Haruna Wakili yana tare da su, yana shiga cikin al’amuransu. Sun yi imanin cewa idan ya samu dama, ba zai yi nesa da su ba, saɓanin yadda wasu wakilan da suka tura a baya suka kasance, waɗanda yawanci ba sa kula da buƙatun al’ummarsu.

Sakamakon kiraye-kirayen da al’ummar Fagge ke yi masa, Hon. Kabiru Haruna Wakili ya amsa cewa da yardar Allah zai fito takarar Majalisar Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Ya roƙi ‘yan jam’iyya, iyaye, jagorori da shugabannin APC na Fagge, maza da mata, da su ba shi haɗin kai da goyon baya domin samun nasara.

Hon. Wakili ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar maslaha, kasancewar al’ummar Fagge ne suka nemi ya fito takara.

Ya ce idan ma an kai ga zaɓen fitar da gwani, yana da yaƙinin cewa al’ummar Fagge za su mara masa baya domin ya samu tikitin APC, sannan a babban zaɓen 2027 za su fito su zaɓe shi.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum