Daga Ibrahim Muhammad Kano
Mazauna jihar Kano na ci gaba da fama da matsanancin ƙarancin ruwa duk da fatan da suka yi cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta kawo ƙarshen wannan matsala da ta daɗe tana addabar jihar.
A wani bincike na musamman da ɗan jarida Sulaiman Ahmad ya gudanar a Kano, an bayyana irin mawuyacin halin da al’ummar jihar ke ciki sakamakon tsananin rashin ruwa.
Binciken ya nuna cewa lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi mulki, mutane da dama a ƙwaryar birnin Kano sun yi fatan cewa nan ba da daɗewa ba za a kawo ƙarshen matsalar ƙarancin ruwa da ta daɗe tana ci wa jama’a tuwo a ƙwarya a jihar.
Sai dai har yanzu ba a magance matsalar ba, maimakon haka ma, sai lamarin ya ƙara ƙamari, abin da ya jefa dubban mazauna cikin takaici.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira biliyan ɗaya wajen ƙoƙarin inganta samar da ruwa a faɗin jihar.
Duk da waɗannan maƙudan kuɗaɗe da aka kashe, sassa da dama na birnin Kano har yanzu ba su da tsaftataccen ruwa mai inganci.
Sakamakon haka, yawancin mazauna na ci gaba da dogaro kacokan ga masu sayar da ruwa domin biyan buƙatunsu na yau da kullum, ciki har da girki, wanka da shan ruwa.
Mazauna da dama sun nuna rashin jin daɗinsu tare da tambayar dalilin da ya sa waɗannan ɗimbin kuɗaɗen da gwamnati ta kashe bai su haifar da wani gagarumin sauyi ba wajen samar da ruwa.
Ci gaba da wannan ƙarancin ruwa ya ƙara jefa iyalai, musamman masu ƙaramin ƙarfi, cikin matsin tattalin arziƙi, domin yanzu suna kashe kaso mai yawa na abin da suke samu wajen siyan ruwa.
Al’umma na kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen matsalar ƙarancin ruwa da ke addabar birnin Kano.







