Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), reshen mazaɓar Bakin Ruwa a ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano, ta sanar da korar Dakta Auwalu Anwar daga cikin jam’iyyar.
Shugaban mazaɓar Bakin Ruwa, Auwalu Abubakar Nuhu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ranar 29 ga Afrilu, 2026.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan zarge-zargen aikata wasu abubuwa da suka saɓa wa dokoki da ƙa’idojin jam’iyyar.
Jam’iyyar ta jaddada cewa hukuncin korar ya fara aiki nan take, tare da gargadin cewa kada a ci gaba da ɗaukar Dakta Auwalu Anwar a matsayin mamba ko wakilin jam’iyyar.
Haka zalika, jam’iyyar ta buƙaci dukkan mambobinta da al’umma da su ci gaba da bin doka da oda domin tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaban jam’iyyar.






