Daga Ibrahim Muhammad, Kano.
Ptll. Marghi Wadzani Adamu, Sarkin Al’ummar Margunawa mazauna Kano, ya taya al’ummar musulmi murnar babbar Sallah.Kuma yayi kira ga cigaba da hada kai da zaman lafiya tsakanin mabambantan addinai da kabilu da ke jihar Kano da kasa baki daya.
Ya taya gwamnatin jihar Kano karkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf murnar Sallah. Ya yabawa gwamnatin kan irin ayyukan cigaba da take aiwatarwa a fannoni daban-daban a jihar.
Sarkin Margunawa ya mika sakon murnar Sallah ga masarautar Kano karkashin jagorancin Khalifa Muhammad Sanusi II. Ya yabawa masarautar bisa kyakkyawan jagoranci wajen hada kan al’umma da kulawa da ake baiwa al’ummarsa ta Marghi.
Ya ce al’ummar Marghi da ke zaune a Kano tun zamanin iyaye da kakanni suna zaune cikin lumana, aminci da auratayya da sauran kabilu. Ya kara da cewa za su ci gaba da bada gudunmawa wajen bunkasa cigaban jihar Kano.
Wadzani Adamu ya yi kira ga iyaye da su bada kulawa da tarbiyya ga ‘ya’yansu domin su zama masu amfani a cikin al’umma. Ya bukace su da su rika gina ‘ya’yansu a kan ilimi da sana’oi na dogaro da kai.
Ga matasa, ya ja hankalinsu da su guji duk wani abu mara kyau da zai cutar da rayuwarsu, kamar shaye-shayen miyagun kwayoyi da daba. Ya kuma gargade su da kada su yarda wasu ‘yan siyasa marasa kishi su yi amfani da su wajen yin abubuwan da ba su dace ba, musamman a gabanin zaben 2027. Ya bukace su da su yi amfani da hankali domin a gudanar da komai cikin zaman lafiya.






