
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ɗan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya na jam’iyyar ADC a ƙaramar hukumar Dala, Ambasada Abdurrahman Mainasara Salga, ya bayyana nasarar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya samu ta zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a matsayin nasara ga duk masu kishin ci gaban Najeriya.
Salga ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya ce nasarar ta zo a daidai lokacin da al’umma ke buƙatar shugabanci nagari domin magance matsalolin tattalin arziki da na tsaro da suka addabi ƙasar.
Ya ce, “A matsayinsa na tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa mai gogewa a harkokin mulki, kuma mutum mai kishin ganin ‘yan Najeriya sun fita daga kangin matsin rayuwa, lokaci ya yi da masu jefa ƙuri’a za su yi nazari cikin natsuwa tare da zaɓar jam’iyyar ADC domin samun sauyi na gaskiya.”
Ya ƙara da cewa nasarar Atiku ta cancanci samun goyon bayan ‘yan Najeriya baki ɗaya, yana mai bayyana fatan cewa al’ummar ƙasar za su bai wa jam’iyyar ADC cikakken goyon baya a babban zaɓen shekarar 2027.
Haka zalika, Ambasada Abdurrahman Mainasara Salga ya yi kira ga sauran ‘yan takarar da suka fafata a zaɓukan fidda gwani na jam’iyyar a matakai daban-daban, ciki har da Majalisar Wakilai, Majalisar Dokokin Jihohi, Majalisar Dattawa da kuma takarar shugaban ƙasa, da su haɗa kai da waɗanda suka samu tikitin takara domin ƙarfafa jam’iyyar da tabbatar da nasararta a zaɓen da ke tafe.
Ya jaddada cewa haɗin kai, haƙuri da sadaukarwa daga dukkan mambobin jam’iyyar ne za su kasance ginshiƙin samun nasarar ADC a zaɓukan shekarar 2027.






