Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugaban Kamfanin Tabarakallah Masha Allah Global, Alhaji Bashir Musa Abdullahi, ya yi kira ga sabbin sarautu huɗu da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sunusi II, ya naɗa da su yi riƙo da gaskiya, adalci da tausayi wajen gudanar da ayyukan sarautun da aka ɗora musu.
Alhaji Bashir ya bayyana hakan ne yayin da yake taya sabbin masu sarautun murnar naɗin da aka yi musu, yana mai cewa amincewa da cancantar da Sarkin Kano ya gani a gare su ne ya sa aka ba su wannan matsayi mai girma.
Ya ce sarauta nauyi ce da ke buƙatar sadaukarwa, haƙuri da kuma kyakkyawar mu’amala da jama’a, don haka ya buƙaci sabbin sarakunan da su ƙara zage damtse wajen kula da harkokin al’umma a matsayinsu na iyaye kuma jagorori.
“Abin da ake buƙata a gare su shi ne su zama abin koyi wajen gaskiya, adalci da tausayi ga talakawa, tare da yin aiki domin haɗin kai da ci gaban al’umma,” in ji shi.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya sanya alheri da albarka a sabbin sarautun, tare da gode wa Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sunusi II, bisa naɗin da ya yi.
“Allah Ya saka masa da alheri, Ya ƙara masa lafiya, hikima da nasara wajen jagorantar Masarautar Kano,” in ji Alhaji Bashir.
Shugaban na Tabarakallah Masha Allah Global ya jaddada cewa kamfaninsa na taya sabbin sarakunan murna tare da yi musu addu’ar samun nasara wajen sauke nauyin da aka ɗora musu da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban Masarautar Kano da al’ummarta baki ɗaya.
Sabbin sarautun huɗun da Mai Martaba Sarkin Kano ya naɗa sun haɗa da:
Hakimin Garun Malam, Ƙachallan Kano
Mayanan Kano
Sarkin Arewa
Barwan Kano
Ya yi fatan Allah Ya ba su ikon gudanar da ayyukansu cikin adalci, gaskiya da tsoron Allah domin amfanin al’umma da martabar masarautar.








