Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) tare da wasu jam’iyyu huɗu, bisa zargin gaza cika wasu sharuɗɗan da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.
Sauran jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP) da Zenith Labour Party (ZLP).
Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin bayan sauraron ƙarar da Ƙungiyar Tsofaffin ’Yan Majalisun Tarayya ta shigar a gaban kotun.
A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026, masu ƙarar sun nemi kotu ta fayyace ko INEC na da wajibcin soke rajistar jam’iyyun siyasa da suka kasa cika sharuɗɗan da Sashe na 225A na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanada, tare da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2022 da kuma ƙa’idojin hukumar.
Masu ƙarar sun bayyana cewa jam’iyyun biyar ɗin sun gaza cika ƙa’idojin da ake buƙata domin ci gaba da kasancewa cikin jerin jam’iyyun siyasa masu rijista a ƙasar.
Daga cikin sharuɗɗan da suka ambata akwai samun aƙalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa a kowace jiha, ko kuma lashe aƙalla kujera ɗaya a zaɓukan tarayya, na jiha ko na ƙaramar hukuma.
Sun kuma yi zargin cewa ADC da sauran jam’iyyun huɗun sun gaza samun wata gagarumar nasara a babban zaɓen shekarar 2023 da kuma zaɓukan cike gurbi da INEC ta gudanar daga baya.
Masu ƙarar sun jaddada cewa ci gaba da barin waɗannan jam’iyyu cikin jerin jam’iyyun siyasa masu rijista ya saɓa wa tanade-tanaden doka, tare da yin barazana ga inganci da sahihancin tsarin zaɓe a Najeriya.
Saboda haka, kotun ta amince da buƙatar masu ƙarar, inda ta bayyana cewa wajibi ne INEC ta ɗauki matakin soke rajistar duk wata jam’iyyar siyasa da ta kasa cika sharuddan da kundin tsarin mulki ya gindaya.






