Na Fito Takarar Sanata A PDP Ne Don Kawo Ingantaccen Wakilci A Kano Ta Tsakiya – Nafi’u Ɗalladi Sankara

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar PDP, Hon. Nafi’u Dalladi Sankara, ya bayyana cewa babban abin da ya sa ya fito takarar kujerar Sanata shi ne domin samar da ingantaccen wakilci da kuma kawo ci gaba ga al’ummar yankin.

Sankara ya ce duk da irin ƙoƙarin da wasu ’yan Majalisar Wakilai na Tarayya daga Kano ta Tsakiya ke yi, har yanzu yankin na fuskantar gibin wakilci a Majalisar Dattawa.

A cewarsa, matasa da sauran al’ummar Kano ta Tsakiya na kallon yadda sanatoci daga wasu yankuna ke samar da damarmaki, ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen ci gaba ga al’ummominsu, amma irin wannan gagarumar gudunmawa ba ta bayyana sosai a Kano ta Tsakiya.

“Wannan ne ya sa muka ga ya dace mu fito mu wayar da kan matasa, mata da dattawanmu cewa akwai buƙatar sake duba irin wakilcin da ake kaiwa Majalisar Dattawa daga Kano ta Tsakiya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa a lokuta da dama, wasu daga cikin waɗanda ake tura wa Majalisar Dattawa daga yankin ba sa zuwa ne bisa tsari da shiri mai kyau, lamarin da ke sa su kasa taka rawar da al’umma ke tsammani daga gare su.

“Idan mutum ya samu damar shiga Majalisa ba tare da cikakken shiri da hangen nesa ba, zai yi wahala ya samar da abubuwan alheri da ci gaban da jama’a ke bukata,” in ji Sankara.

Hon. Sankara ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin tsofaffin gwamnoni da suka wakilci yankin a Majalisar Dattawa ba su nuna irin jajircewar da ake buƙata wajen nemo wa al’umma damarmakin ci gaba ba.

“Sau da yawa ana rasa damarmaki masu yawa da za su amfani al’umma saboda rashin ƙwazo da rashin bin diddigin abubuwan da suka kamata a Majalisa. A matsayina na wanda ya fahimci yadda harkokin Majalisa ke gudana, na san akwai damarmaki masu yawa da za a iya jawo wa Kano ta Tsakiya idan aka samu wakilci nagari,” in ji shi.

Ya ce yana da ƙwarewa da gogewa a harkokin majalisa, tare da fahimtar hanyoyin da za a bi wajen samar da ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen tallafa wa matasa, mata da sauran al’umma.

Da yake magana kan jam’iyyarsa ta PDP, Hon. Nafi’u Dalladi Sankara ya ce jam’iyyar ba bakuwa ba ce a Jihar Kano, domin ta taɓa aiwatar da ayyukan ci gaba da har yanzu al’ummar jihar ke alfahari da su.

“PDP jam’iyya ce da ta bar tarihi mai kyau a Kano. Saboda haka muna da yakinin cewa al’umma za su sake ba ta dama domin ci gaba da gina jihar da kuma ƙasa baki ɗaya,” in ji shi.

  • Related Posts

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Sakamakon irin dimbin alheri da gudummawar da dan takarar majalisar tarayya na PDP, Hon. Alhaji Abubakar Ibrahim Maina, ke bai wa al’ummar karamar hukumar Tarauni, al’ummar…

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo