Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara ya fara haskawa a fagen siyasa tun daga matakin tushe, inda ya samu karɓuwa a tsakanin al’ummarsa tun daga mazaba har zuwa Ƙaramar Hukumar Gezawa.
Wannan karɓuwa ta samo asali ne sakamakon kusancinsa da talakawa da kuma jajircewarsa wajen magance matsalolin da suka addabi yankin.
Ya riƙe muƙamin Shugaban Ƙaramar Hukumar Gezawa, inda a lokacin mulkinsa ya mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa da suka haɗa da samar da ruwan sha, gyaran makarantu, inganta harkokin kiwon lafiya, ƙarfafa matasa ta hanyar sana’o’i, da kuma samar da guraben ayyukan yi.
Salon shugabancinsa na buɗe ƙofa ga jama’a ya ƙara masa farin jini a faɗin gundumomi 11 na ƙaramar hukumar.
Sakamakon irin ayyukan ci gaba da ya gudanar a matsayin shugaban ƙaramar hukuma, jama’a da jam’iyyarsa suka mara masa baya wajen neman kujerar ɗan majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar mazabar Gezawa. Daga bisani ya yi nasara a zaɓe, lamarin da ya ba shi damar shiga majalisar.
A majalisar dokokin jihar, Hon. Tsamiyar Kara ya kasance cikin ‘yan majalisar da suka taka muhimmiyar rawa wajen kare muradun al’ummarsu. Duk da yanayin siyasar da ake ciki a lokacin, ya ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare haƙƙoƙin mazaɓarsa tare da gabatar da ƙudurori da suka shafi ilimi, aikin gona, samar da ayyukan yi da sauran batutuwan da suka shafi ci gaban al’umma.
An san Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara a matsayin ɗan siyasa mai sauƙin kai, mai kusanci da jama’a, kuma mai sauraron koke-koke da buƙatun al’ummarsa. Wannan ya sa yake ci gaba da kasancewa cikin zukatan mutanen da yake wakilta.
Yanzu haka, ya shafe kusan shekaru uku yana wakiltar al’ummar Gezawa a Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Bisa ga yadda ake bayyana gamsuwa da irin rawar da yake takawa a majalisar, masu ruwa da tsaki da dama a yankin sun nuna goyon bayansu ga ci gaba da wakilcinsu da yake yi, tare da bayyana shi a matsayin wanda ya dace ya sake neman kujerar majalisar a zaɓen shekarar 2027.
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Gezawa sun bayyana Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara a matsayin mutum mai kyakkyawar alaƙa da jama’a, mai mutunta kowa da kowa, kuma mai ƙoƙarin ganin an samu ci gaba mai ɗorewa a yankin.
A cewarsu, irin ayyukan da ya gudanar da kuma kusancinsa da al’umma sun sa suka ɗauke shi a matsayin wanda ya cancanci a sake ba wa damar ci gaba da wakiltarsu a Majalisar Dokokin Jihar Kano ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.






