Daga Ibrahim Muhammad Kano
Wani jigo a jam’iyyar ADC ya musanta rahotannin da ke cewa jam’iyyar ta tabbatar da Malam Ibrahim Khalil a matsayin halastaccen ɗan takararta na gwamnan Jihar Kano a zaɓen shekarar 2027.
Wannan na zuwa ne bayan da wasu da ke iƙirarin shugabannin riƙon ƙwarya na jam’iyyar ADC a jihar Kano, tare da wasu masu ruwa da tsaki, suka gudanar da taron manema labarai inda suka bayyana cewa sun amince da Ibrahim Khalil a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar.
Sai dai, wata majiya mai tushe a cikin jam’iyyar ADC ta ƙasa, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa waɗanda suka yi wannan sanarwa ba su da hurumin yanke irin wannan hukunci a madadin jam’iyyar.
“A halin yanzu, jam’iyyar ADC ba ta da sahihin shugabanci a jihar Kano. Wa’adin shugabannin riƙon ƙwarya ya ƙare tun ranar 19 ga watan Mayu, kuma uwar jam’iyyar na ƙasa ce ke shirye-shiryen naɗa sababbin shugabannin riƙo. Saboda haka, duk wata sanarwa da aka fitar dangane da tabbatar da ɗan takara ba ta da tushe,” in ji majiyar.
Majiyar ta kuma jaddada cewa har zuwa yanzu jam’iyyar ADC ta ƙasa ba ta bayyana ko tabbatar da kowane mutum a matsayin ɗan takararta na gwamnan Jihar Kano ba.
Ƙoƙarin jin ta bakin shugabannin jam’iyyar ADC na ƙasa domin samun karin haske kan batun bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
A halin yanzu, daga cikin fitattun masu neman tikitin gwamnan jam’iyyar ADC a Kano akwai Alhaji Ibrahim Al-Amin Little da Malam Ibrahim Khalil, waɗanda ake ganin suna daga cikin manyan jiga-jigan da ke zawarcin tikitin jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.






