Mairiga Ya Gargadi ‘Yan Takarar NDC Kan Sanya Duk Wani Kuɗi Da Ba Na Asusun Jam’iyyar Ba

Daga Ibrahim Muhammad, Kano.

Shugaban jam’iyyar NDC na Jihar Kano, Hon. Husaini Isa Mairiga, ya gargaɗi duk ‘yan takarar jam’iyyar a kowane mataki da su guji biyan wani kuɗi a cikin wani asusu da ba na uwar jam’iyyar NDC ta ƙasa ba ko na jam’iyyar NDC ta Jihar Kano ba.

“Duk wanda ya saka kuɗi a wani asusu da ba waɗannan ba, to ya sani ya biya kuɗinsa a banza,” in ji Mairiga a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi da yamma a Kano.

Ya kuma ja hankalin ‘yan takarar da ke ganin sun fi ƙarfin jam’iyya, yana mai cewa ranar da hukumar zaɓe ta ƙasa za ta fitar da sunaye ne za su gane cewa “jam’iyya ce uwar kowa.”

“A matsayina na halastaccen shugaban NDC na Kano, duk ɗan takarar da ya ce ba zai bi umarninmu ba, yana ganin ya isa, to za mu buga da shi, sai ya gani,” in ji Hon. Mairiga.

Ya ƙara da cewa babu wani ɗan takara da zai karɓi fom ba tare da ya biya kuɗin fom ɗin nuna sha’awa da na nomination ba, waɗanda za a miƙa su ga uwar jam’iyya ta ƙasa.

Haka kuma, ya ce wajibi ne kowane ɗan takara ya biya administrative charges da consultation charges a cikin asusun jam’iyyar NDC na Jihar Kano kaɗai.

“Idan ba asusun NDC na Kano ba ne, to ka sani ka biya kuɗinka a banza. Domin mu ne kaɗai aka sani a matsayin halastattun shugabannin jam’iyyar a Kano,” in ji shi.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum