Masu Amfani da Shafukan Sada Zumunta Su Riƙa Tantance Sahihan Labarai Kafin Wallafawa -Abdulaziz Abdulaziz

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga masu amfani da shafukan sada zumunta da sauran masu yaɗa labarai da su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin wallafa su, domin kare zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Kiran ya fito ne daga Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa na Musamman kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Abdulaziz Abdulaziz, a jawabin maraba da ya gabatar yayin buɗe taron farko na Arewa Media Summit da aka gudanar ranar Litinin a Kano.

Abdulaziz ya ce bunƙasar dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa na buƙatar haɗin gwiwa da amincewa tsakanin gwamnati, kafafen yaɗa labarai da kuma al’umma.

Ya bayyana taron a matsayin wani dandali da ya haɗa shugabanni, ‘yan jarida, masu tasiri a shafukan sada zumunta da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin ƙarfafa alaƙar gwamnati da jama’a ta hanyar gaskiya, riƙon amana da kuma bin ƙa’idodin aikin jarida.

Ya ce taken taron na bana, “Government-Citizen Accord: Accountability, Responsibility and Ethical Media Practice,” ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar sake gina amincewa tsakanin gwamnati da al’umma.

A cewarsa, gwamnati na da alhakin buɗe ƙofofin samun bayanai, yayin da al’umma ke da nauyin tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su, tare da riƙe gwamnati da alhakin ayyukanta cikin lumana.

Ya ƙara da cewa kafafen yaɗa labarai su ne gada tsakanin gwamnati da jama’a, kuma ingantaccen aikin jarida da tabbatar da sahihancin labarai na taka muhimmiyar rawa wajen gina zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.

Abdulaziz ya jaddada cewa masu tasiri a shafukan sada zumunta sun zama manyan masu yaɗa bayanai a wannan zamani, saboda haka wajibi ne su riƙa tantance gaskiya kafin wallafa duk wani saƙo.

“A yau, saƙon da aka wallafa na iya haifar da rikici ko tayar da husuma cikin ƙanƙanin lokaci. Don haka bai kamata neman farin jini ko ƙarin masu kallo ya zama sanadin jefa ƙasa cikin tashin hankali ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, yayin da babban zaɓen shekarar 2027 ke ƙaratowa, akwai buƙatar masu amfani da shafukan sada zumunta su ɗauki kansu a matsayin masu kare zaman lafiyar al’umma, tare da gyara duk wani kuskure idan ya faru.

A wani ɓangare na shirye-shiryen taron, Abdulaziz ya bayyana cewa an horas da sama da mutum 100 daga cikin masu goyon bayan jam’iyyar APC da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan dabarun yaɗa bayanai da bayyana manufofi da nasarorin gwamnati yadda ya kamata.

Ya kuma ce an ƙaddamar da shirin “Gani-Ya-Kori-Ji”, wanda zai zagaya jihohin Arewacin Nijeriya domin duba tare da haska ayyukan ci gaba da Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi suka aiwatar.

A cewarsa, taron ya nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kare ‘yancin faɗin albarkacin baki, ƙarfafa tattaunawa da kuma bunƙasa dimokuraɗiyya.

Ya ce an shirya taron ne domin bai wa mabambantan ra’ayoyi da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya damar tattaunawa kan makomar alaƙar gwamnati da jama’a.

A ƙarshe, Abdulaziz Abdulaziz ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa amincewa da karɓar baƙuncin taron.

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum