Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa horon da ake bai wa akantoci zai taimaka wajen ƙara inganta ayyukansu tare da ƙara musu ilimi da ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan gwamnati.
Kwamishinan Kasafi na Jihar Kano, Hon. Musa Sulaiman Shanono, ne ya bayyana hakan a madadin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf lokacin da ya buɗe taron ƙungiyar ANAN na shiyyar Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Kano.
Ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin ma’aikata da dama domin samun horo a fannin ilimin akanta, inda da dama daga cikinsu suka kammala karatunsu.
Ya ƙara da cewa, a halin yanzu ma akwai wasu da dama da gwamnati ke ci gaba da ɗaukar nauyinsu domin samun irin wannan horo.
“Gwamna Abba Kabir Yusuf koyaushe yana a shirye wajen bayar da gudunmawa don ƙara wa ma’aikata ilimi, domin ilimi ne ginshiƙin gudanar da ayyukan gwamnati cikin ƙwarewa da nagarta,” in ji shi.
Hon. Musa Sulaiman Shanono ya kuma yi fatan mahalarta taron za su mayar da hankali wajen cin gajiyar darussan da za a gabatar, domin su yi amfani da ilimin wajen inganta ayyukansu a jihohinsu.
A jawabinsa, Shugaban Ƙungiyar ANAN na Ƙasa, reshen Jihar Kano, Muhammad Abba Aliyu, ya ce za a rantsar da sabbin mambobin ƙungiyar 1,500 a yayin taron ANAN na shiyyar Arewa maso Yamma, wanda Jihar Kano ta karɓi baƙuncinsa.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ANAN na gudanar da irin wannan taro sau shida a shekara a faɗin ƙasar nan, kuma a wannan karo an gudanar da na shiyyar Arewa maso Yamma a Kano.
“Wannan taro na horarwa ne ga akantoci domin ƙara inganta aikinsu da bunƙasa ƙwarewarsu,” in ji Muhammad Abba.
Shi kuma Mai Magana da Yawun ANAN na Ƙasa, reshen Jihar Kano, Isma’il Salisu Gurjiya, ya ce ƙungiyar na horar da akantoci ne kan hanyoyin ƙara ƙwarewa wajen gudanar da harkokin sana’a, ayyukan ofis da sauran fannoni na aikin akanta.
Ya bayyana gamsuwarsa da yadda taron ke gudana a Kano, inda ya ce ƙwararru suka gabatar da muhimman bayanai da za su taimaka wajen bunƙasa harkar akanta.
Isma’il Salisu Gurjiya ya ce har yanzu ana fama da ƙarancin ƙwararrun akantoci a ƙasar nan, amma ANAN na ci gaba da bayar da horo domin ƙara yawan ƙwararru a fannin.







