Daga Ibrahim Muhammad Kano
Sabuwar Sakatariyar Dindindin a Gwamnatin Jihar Kano, Hajiya Hauwa Nuhu Wali, wacce ta kasance Shugabar Makarantar GGC Dala, ta yiwa sabbin shugabanin kungiyar “ANCOPSS” fatan alkhairi, tare da kira gare su da su gyara kurakuran da aka samu a baya da kuma aiki tare da hadin kai.
Hajiya Hauwa ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa davyan.jarida a taron kaddanar da sabbin shugabannin kungiyar shugabannin makarantun sakandire na jihar Kano.
Ta ce a lokacin da tayi wani taro a wani lokacin a baya a GGC Dala ta bayyana wasu nasarorin da makarantar ta samu, tare da nuna matsaloli biyu da suke fuskanta. Daga cikin matsalolin akwai bukatar karin gadaje nabkqanan.dalibai da kuma tallafin magunguna.
Ta bayyana cewa tana da yakinin cewa kafin karshen zangon karatu da zasu tafi hutu, da yardar Allah za a samu tallafin magunguna daga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf
“Gashi yanzu an samar, kuma ni ma na kasance daga cikin wadanda suka karbi tallafin magunguna na makarantar GGC Dala kafin na bar makarantar, inji ta.
Hajiya Hauwa ta ce babu abin da za su iya cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf sai addu’a.
“Muna addu’ar Allah ya ba shi tukuici da Aljanna, kuma Allah ya maimaita masa nasara a zaben 2027,” ta kara da cewa.
Ta kuma gode wa Ma’aikatar Ilimi karkashin jagorancin Kwamishina, Hon. Gwani Ali Haruna Makoda.da Sakataren Dindindin na Ma’aikatar, Kwamared Bashir Baffa, da Sakataren Hukumar Makarantun Sakandare, Alhaji Rabiu Saleh Gwarzo tare da Shiyyar Ilimi ta Dala/Gwale. Ta ce za ta ci gaba da ba su hadin kai duk inda ta ke.
Game da sabon mukamin da aka ba ta na Sakataren Dindindin, Hajiya Hauwa Nuhu Wali ta ce ba ta da abin da za ta ce sai godiya.
“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi mana abin da a tarihi ba a taba yi ba. Shi mutum ne da ke da kishin ilimi a zuciyarsa tun yana Kwamishina,” inji ta.
“Yanzu da Allah ya kawo shi Gwamna, ya sanya ilimi a matsayin manufofinsa na farko, na biyu da na uku. Saboda haka ba mu da bakin da za mu iya yi masa godiya sai Allah yasa ya gama wa’adinsa lafiya.”
Ta kara da cewa su a matsayinsu na Sakatarorin dindindin zasu baiwa Gwamnan cikakken hadin kai wajen inganta ilimi da tabbatar da nasararsa dari bisa dari. “A zaben 2027 mai zuwa ba za mu ba shi kunya ba. Za a yi zabe ya yi nasara, kuma Allah zai maimaita masa da yardar Allah,”







